Rayukan Mutum 10 Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Kwara

Rayukan Mutum 10 Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota a Jihar Kwara

  • An samu asarar rayuka bayan wasu motoci biyu sun yi taho mu gama da safiyar ranar Litinin a jihar Kwara
  • Mummunan hatsarin motan wanda ya ritsa da wata babbar mota wata motar bas ya jawo mutum 10 sun rasa rayukansu
  • Hukumar FRSC wacce ta tabbatar da aukuwar hatsarin ta ce wasu mutum 10 kuma sun samu raunuka daban-daban a sakamakon hatsarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Aƙalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya auku a safiyar ranar Litinin a ƙauyen Iyemoja kusa da titin Oloru-Okoolowo a ƙaramar hukumar Moro ta jihar Kwara.

Jaridar Nigerian Tribune ta tattaro cewa hatsarin wanda ya auku da misalin ƙarfe 06:40 na safe ya ritsa da motoci biyu, wata babbar motar ƙirar Volvo da wata motar bas ƙirar Toyota Hiace.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta fara binciken minista kan badakalar N585.2m

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Kwara
Mutum 10 sun rasa rayukansu a hatsarin mota a Kwara Hoto: @FRSCNigeria
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta ce hatsarin ya ritsa da mutum 20 (manyan maza 15, manyan mata huɗu da yaro namiji ɗaya), inda manya maza 10 suka samu raunuka daban-daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutum 10 da suka rasa ransu a hatsarin sun haɗa da manyan maza mutum biyar, manyan mata mutum huɗu da yaro namiji ɗaya.

Me hukumomi suka ce a kan hatsarin?

Kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kwara, Stephen Dalung, ya tabbatar da aukuwar hatsarin a cikin wata sanarwa.

Ya bayyana cewa binciken farko da jami'an hukumar suka gudanar, ya nuna cewa hatsarin ya faru ne a bisa wucewar ganganci da direban babbar motar Volvo ya yi wanda hakan ya haddasa ya yi karo da motar bas ɗin.

Hukumar ta FRSC ta kuma ce motar bas din ta taho ne daga Legas a kan hanyar zuwa Sokoto kuma tana ɗauke fasinjoji 17 da kayayyakinsu, yayin da babbar motar ta taho daga Arewa a kan hanyar zuwa Legas inda take ɗauke da fasinjoji uku.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga har fada sun yi awon gaba da babban basarake

Kwamandan ya bayyana cewa tuni aka kai waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Ilorin yayin da aka kai gawarwakin mamatan daƙin ajiye gawa na asibitin koyarwa na jam'iar Ilorin (UITH) da ke Ilorin.

Tirela Ta Murƙushe Ɗan Sanda

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jami'in ɗan sanda ya gamu da ajalinsa bayan babbar motar tirela ta murkushe shi a jihar Jigawa.

Lamarin ya faru ne kan hanyar Kano zuwa Hadejia a karamar hukumar Ringim, lokacin da jami'in ɗan sandan yake binciken ababen hawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel