Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Mutumin da Ya Sace Alkur'anai a Masallaci, Ta Ba Shi Zaɓi 1 a Abuja

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Mutumin da Ya Sace Alkur'anai a Masallaci, Ta Ba Shi Zaɓi 1 a Abuja

  • Kotu ta ɗaure lebura tsawon watanni 15 a gidan gyaran hali bayan kama shi da laifin satar Alƙur'ani a wani Masallaci da ke Abuja
  • Alkalin kotun mai zama a Abuja, mai shari'a Malam Aliyu Kagarko, ya bai wa mutumin mai suna, Terkaa Akishi, zaɓin tarar N40,000
  • Tun farko mai gabatar da kara daga hukumar ƴan sanda ya ce sun kwato kayayyakin da mutumin ya sace yayin gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wata kotun Grade 1 mai zama a Lugbe, babban birnin tarayya Abuja, ta yanke wa wani lebura, Terkaa Akishi (36), hukuncin ɗaurin watanni 15 a gidan yari.

Kotun ta yanke wa mutumin wannan hukunci ne ranar Talata bayan kama shi da laifin satar Alƙur'nai da wayar hannu a masallaci a Asokoro, cikin birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Okuama: Bola Tinubu ya gana da gwamnan PDP kan kisan sojoji 17, sahihan bayanai sun fito

Kotu ta yanke hukunci.
An ɗaure lebura wata 15 kan satar alkur'ani a Abuja Hoto: Court of appeal
Asali: UGC

Mai Shari'a Malam Aliyu Kagarko ne ya ɗaure mutumin bayan ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin ya kuma ba shi zaɓin tarar N40,000 kuma bayanai sun nuna tun farko an gurfanar da Mista Akishi ne kan tuhumar shiga gonar da ba tasa ba da sata.

Yadda zaman shari'ar ta gudana

Mai shigar da ƙara, Mista Emeka Ezeganya, ya ce an kai rahoton abin da wanda ake zargi ya aikata ga ƴan sandan caji ofis na Asokoro.

A cewarsa, Mista Isah Balikisu na dakarun sojojin Guards Birged na rundunar sojin kasa da ke Asokoro a Abuja ne ya kai rahoton ga ƴan sanda ranar 14 ga Maris.

Mai gabatar da kara ya ce har yanzu ba a tantance darajar kuɗin kayayyakin da wanda ake tuhuma ya sace ba.

Kara karanta wannan

FCT: An tafka ɓarna yayin da mutane ke tsaka da sallar tarawihi a watan azumin Ramadan

Sai dai ya faɗawa kotun cewa jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kwato Alƙur'anan da wayar guda ɗaya daga hannun Akishi a lokacin da suke bincike.

Mai gabatar da kara ya ce laifuffukan da ake tuhumar mutumin sun ci karo da sashe na 348 da 287 na kundin laifuffuka Final Kod, a rahoton jaridar Pulse.

Kotun tarayya ta ƙi aminta da rokon Shaibu

A wani rahoton kuma mataimakin gwamnan jihar Edo ya yi rashin nasara a babbar kotun tarayya yayin da yake kokarin hana majalisar dokoki tsige shi.

Alkalin kotun, mai shari'a James Omotoso, ya ƙi aminta da ko ɗaya daga cikin buƙatun Kwamared Philip Shaibu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel