A madadin yi wa budurwa 'Ramadan Basket', matashi ya sa mahaifiyarsa kukan daɗi

A madadin yi wa budurwa 'Ramadan Basket', matashi ya sa mahaifiyarsa kukan daɗi

  • Wani faifan bidiyo da ya ja hankalin mutane ya nuna yadda wani matashi ya aikawa mahaifiyarsa kyautar kudi da ya ba ta mamaki
  • Mahaifiyar ta nuna matukar jin dadinta akan abin da danta ya yi ta hanyar aika masa da sakon murya mai tsuma zuciya
  • A cikin sakonta mai ratsa zuciya, ta yi addu'ar ubangiji ya albarkaci aikin da danta yake yi da kuma fatan samun ci gaba a rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wani faifan bidiyo ya nuna irin shaukin da wani matashi ya jefa mahaifiyarsa a ciki bayan da ya aika mata kudi a matsayin kyautar watan Ramadan, al'amarin da ya dauki hankulan mutane a yanar gizo.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya girgiza Intanet ta hanyar daga buhun shinkafa da hakoransa

Mahaifiyar da ta nuna matuƙar jin dadinta kan wannan kyautar ba zata, ta aika masa da sakon murya mai tsuma zuciya.

Mahaifiya ta aika wa yaronta sako mai ratsa zuciya
Mahaifiyar matashin ta cika da farin ciki bayan ganin kyautar kudin da ya aika mata. Hoto: @jicoblack
Asali: TikTok

Muhimmancin kyautatawa iyaye

A cikin sakonta mai ratsa zuciya, ta yi masa addu’ar samun nasara a dukkan al’amuransa tare da bayyana fatanta na samun ci gabansa a rayuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan labarin mai daɗi, kamar yadda @jicoblack ya wallafa a Tik Tok, ya zama abin tunatarwa ga matasa da su tuna da iyayensu a wannan lokaci maimakon aika wa budurwa 'Ramadan basket'.

Haka nan kuma yana nuna muhimmancin tunawa da na-kusa da kai domin ba su tallafi a wannan watan Ramadan, wanda zai sa ka samu tarin lada daga Allah (S.W.A).

Kalli bidiyon da ke ƙasa:

Ra'ayoyin jama'a

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a kan wannan bidiyo:

Kara karanta wannan

Yadda za a bi a maido Dalar Amurka N160 daga N1600 Inji Masanin tattalin arziki

User928399373933838 ya ce:

"Ya fi kyau in bai wa iyayena kudi fiye da in bai wa budurwar da ban aura ba, Allah ya yi mahaifiyarka tsawon rai."

YEKINI ya rubuta cewa:

"Walahi wannan shi ne abin da Annabi ya bayyana a matsayin abun albarka da nasara a rayuwa. Idris Ayinde ba za ka taba kashe kuɗinka a kan rashin lafiya ba."

Cranberry2 ta ce:

"Amin, amma don Allah bai dace ace kowa sai ya san sunan mahaifiyarka ba."

Ita kuwa Temitopeoluwa716 ta rubuta:

"Wannan irin mahaifiyata ce, wasu lokutan idan ta fara yi mun addu'a sai na ce mata ta dakata haka nan. Allah ya albarkaci iyayen kwarai da 'yayansu."

Lokutan azumi a fadin duniya

A wani rahoton na daban, Legit Hausa ta yi cikakken bayani game da lokutan azumi a kasashen duniya, yayin da ake gudanar da zumin Ramadan na shekarar 1445.

Wannan rahoton zai taimaka wajen ilimantar da Musulmi kan lokutan sahur da buda baki a kasashe daban-daban da kuma wasu hukunce-hukunce da suka shafi azumi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel