Kano: Sabuwar Takaddama Ta Taso Yayin da 'Yan Sanda Suka Bukaci Diyya Daga Murja Kunya

Kano: Sabuwar Takaddama Ta Taso Yayin da 'Yan Sanda Suka Bukaci Diyya Daga Murja Kunya

  • Yayin da ake ci gaba da shari'ar fitacciyar 'yar Tiktok, Murja Ibrahim, rundunar 'yan sanda ta shigar da ita kara
  • Jami'an 'yan sandan sun bukaci Murja ta biya su diyyar N500,000 kan shigar da ita kara da Murja tayi ba tare da laifin komai ba
  • Rundunar ta shigar da korafin ne gaban babbar kotun jihar Kano inda ta bukaci a cire sunanta a cikin wadanda ake kara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Rundunar ’yan sanda a jihar Kano ta bukaci fitacciyar 'yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya da ta biya ta diyyar N500,000.

Rundunar ta nemi wannan bukata ne bayan shigar da korafi gaban babbar kotun jihar, cewar jaridar Aminiya.

Kara karanta wannan

Kaduna: Rundunar soji ta samu gagarumar nasara bayan ceto mutane 16 hannun miyagu

Yan sanda na neman diyya daga Murja Kunya a Kano
Rundunar 'yan sanda ta bukaci diyyar N500,000 daga Murja Kunya. Hoto: @KanoPoliceNG, Murja Ibrahim Kunya.
Asali: Twitter

Dalilin rundunar na neman diyya daga Murja

'Yan sandan na zargin jarumar da maka su a kotu ba tare da sun aikata mata laifin komai ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne bayan an gurfanar da Murja a gaban kotu kan yada badala da kuma bata tarbiyar yara a jihar.

Lauyan rundunar, Barista Abdussalam Saleh ya bukaci kotun ta cire sunan hukumar a jerin wadanda ake kara.

"Ba mu san abin da ake karar mu a kai ba a ɓangarorin biyu ganin cewa ba a kawo korafin da zamu gayyaci kowa ba."
"Tabbas duk abin da aka kawo wa kotu babu gaskiya a cikin kowane ɗaya daga ciki."

- Barista Abdussalam Saleh

Cece-kuce tserewar Murja daga gidan yari

A wani labarin, an yi ta cece-kuce kan cewa fitacciyar 'yar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya ta tsere daga gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Mataki mai karfi da hukumar soji ta dauka a Delta bayan kashe mata jami'ai 16

Mutane da dama na zargin gwamnatin jihar Kano da hannu a cikin sakin matashiyar wanda ya fara saka shakku a zukatan mutane.

Malami ya shawarci Abba Kabir kan Murja

Kun ji cewa, fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil ya shawarci Gwamna Abba Kabir ya ba Murja Ibrahim Kunya mukami a gwamnati.

Shehin malamin ya bukaci a ba ta mukamin hadima a bangaren sadarwa domin hana ta yin abubuwan da ta ke yi a cikin al'umma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel