An Cafke Babban Lauya da Zargin Kin Biyan 'Yar Gidan Magajiya Bayan Sun Gama Lalata

An Cafke Babban Lauya da Zargin Kin Biyan 'Yar Gidan Magajiya Bayan Sun Gama Lalata

  • Dara ta ci gida yayin da babban lauya ya shiga hannun hukuma inda aka garkame shi a kotu kan zargin cin zarafin budurwa
  • An zargin lauyan mai suna Emmanuel Ekunife da yaudarar karuwa inda ya kwanta da ita ba tare da biyanta hakkinta ba a Abuja
  • Lauyan bayan isa ofishin 'yan sanda da aka yi kararsa, ya fara nadan faifan bidiyo wanda ya kara jefa shi cikin matsala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An tunkuda keyar wani babban lauya a birnin Abuja zuwa kotu kan zargin kin biyan karuwa kudinta bayan lalata da ita.

Lauyan mai suna Emmanuel Ekunife ana zargin ya ci zarafin budurwa da kuma kin biyanta hakkinta.

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

Lauya ya shiga hannun 'yan sanda bayan kin biya karuwa hakkinta
Ana zargin lauyan da cin zarafin budurwar bayan amfani da ita. Hoto: Nigerian Police Force.
Asali: Twitter

Yaushe lamarin ya faru da Abuja?

Lamarin ya faru ne bayan macen mai zaman banza mai suna Queeneth John ta kai kara ofishin 'yan sanda a ranar 12 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Queeneth ta ce a ranar 11 ga watan Maris Emmanuel ya bukaci su je otel din Bannex inda ya kwanta da ita amma ya ki biyanta kudi har ma ya ji mata rauni.

Tribune ta tattaro cewa lauyan ya kara dagula lamarin bayan fara nadar faifan bidiyon jami'an 'yan sanda a ofishinsu.

Matakin da alkalin kotun ya dauka kan lauyan

Yayin da aka ci gaba da bincike, Emmanuel ya tabbatar da aikata hakan da kuma karin wasu laifuffuka inda aka dauki bayanansa, cewar Newstral.

Daga bisani mai Shari'a, Aliyu Kagarko ya ba da belin lauyan kan kudi Naira miliyan 1 da wadanda za su tsaya masa.

Kara karanta wannan

"Ka canja mani rayuwa": Bature ya bai wa dalibin Najeriya naira miliyan 159 da sabuwar mota

Har ila yau, alkalin kotun ya dage ci gaba da sauraran karar har sai ranar 18 ga watan Afrilu domin kara bincike kan batun.

An garkame hadimin tsohon gwamna

Kun ji cewa Mai dafa abinci ga tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode ya shiga matsala bayan garkame shi a gidan kaso na tsawon kwanaki 30.

Ana zargin Victor Abayomi da satar kayayyakin tsohon gwamnan na miliyoyin kudi a gidansa da ke Ikoyi.

Ana zarginsa da hadin baki da wasu mutane inda suka sace kayan inda daga bisani aka cafke shi a jihar Osun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel