Yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 60 a sabon hari da suka kai jihar Zamfara
- Kuma dai, an sake kai hari karamar hukumar Bakura a jihar Zamfara
- Yan bindiga sun yi awon gaba da kimanin mutane 60
- Kwamishanan labaran jihar ya tabbatar da hakan ga manema labarai
Zamfara - An yi awon gaba da dimbin mutane sakamakon mumunan harin da tsagerun yan bindiga suka kai garin Rimi, a karamar hukumar Bakura jihar Zamfara, ranar Juma'a.
Kwamishanan labaran jihar Zamfara, Ibrahim Dosara, ya tabbatar da hakan ranar Juma'a.
A cewarsa, an yi garkuwa da kimanin mutum 60 amma jami'an tsaro basu tabbatar da adadin ba.
A hirar da yayi da gidan talabijin TVC, yace:
"Da safen nan, mun tashi da labarin cewa yan bindiga sun kai hari garin Rimi a karamar hukumar Bakura, inda sukayi awon gaba da mutane 60, duk da cewa ba'a tabbatar ba."
"Jami'an tsaro da jami'an gwamnati na iyakan kokari wajen sanin ainihin adadin wadanda aka sace da wadanda aka kashe."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Karamar hukumar Bakura, gaba dayanta hanya ce ga yan bindiga zuwa Dansadau, Birnin Gwari da sauran sassan jihar Neja."
Wannan ya biyo bayan sace daliban makarantar noma da aka sace ranar Litinin, 16 ga Agusta, 2021.
Yan bindigan sun yi awon gaba da dalibai da Malamai da yawa da har yanzu ba'a san adadinsu ba.
Rijistran makarantar, Aliyu Bakura, ya tabbatar da hakan ga BBC Hausa da safiyar Litinin.
Ya ce masu gadi uku da dan sanda 1 aka kashe.
Za'a sakosu nan da kwana 2
A cewar Dosara, gwamnatin jihar na sa ran za'a saki daliban nan kwanaki biyu.
Yace:
"Tsakani da Allah, gwamnatin jihar Zamfara, tare da jami'an tsaro na dukkan kokari don tabbatar da cewa an saki dalibai da malaman."
"Muna sa ran cewa na da kwana 2, yan bindigan zasu sake daliban."
Asali: Legit.ng