Bashin Dalibai: Tinubu Ya Bayyana Ranar Da Zai Kaddamar Da Shirin Ba Dalibai Rancen Kudi

Bashin Dalibai: Tinubu Ya Bayyana Ranar Da Zai Kaddamar Da Shirin Ba Dalibai Rancen Kudi

  • Gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta yi karin haske kan jinkiri da aka samu wajen kaddamar da tsarin ba dalibai rancen kudi
  • Dr Akintunde Sawyerr, sakataren shirin na NELFund, ya yi kira ga dalibai da suka cancanta da su je su yi rijista a shafin yanar gizo da za a bude a wannan matan na Maris
  • Ya ce tun farko an samu jinkiri wajen aiwatar da shirin ne domin suna ta kokarin ganin an dauki matakan da suka dace don tsarin ya tafi daidai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Abuja - Gwamnatin tarayya ta tsayar da watan Maris domin kaddamar da shafin yanar gizo na bayar da lamunin karatu ga daliban da suka cancanta.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai hari makaranta, sun dauke yaran firamare

Babban sakataren shirin na NELFund, Dr Akintunde Sawyerr, ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, a Abuja.

Gwamnatin Tinubu ta yi karin haske kan tsarin ba dalibai rancen kudi
Tsarin ba dalinbai rancen kudi zai fara aiki a wanan nan na Maris Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sawyerr ya bukaci daliban da suka cancanta da su yi rijista don samun rancen kudin, jaridar Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa aka samu jinkiri wajen fara shirin?

A ranar 12 ga watan Yunin 2023, Shugaban kasa Bola Tinubu ya sanya hannu kan tsarin bai wa dalibai musamman marasa karfi rancen kudi don su yi karatu a duk makarantar da suke so.

Ya kamata tsarin ya fara aiki tsakanin Satumba da Oktoban 2023, amma saboda wasu dalilai, aka mayar da shi watan Janairu.

Da yake bayyana dalilan da suka sa aka samu jinkiri wajen fara shirin kamar yadda aka tsara tun da farko, Sawyerr ya ce abu ne na fasaha kuma ana bukatar samar da matakan da suka dace don aiwatar da su yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Buga kudi: Yadda Buhari ya jawo hauhawar farashin kaya, Ministan Tinubu ya magantu

"A watan nan na Maris za a kaddamar da shirin, kuma dalilin jinkirin da aka samu shine cewa muna kokarin yin abubuwan da suka kamata.
“Wannan ba shiri ne na siyasa ba inda za mu ce, kawai za mu yi shi ne, duk yadda ya kasance daidai ne."

- Sawyerr

Tinubu zai inganta ilimin marasa gata

Ya jaddada cewa wannan shiri ne da suke son ganin ya tafi yadda ya kamata, don haka dole su yi abin da ya dace kuma yake daidai.

Sawyerr ya kuma sake jaddada jajircewar Shugaban kasa Bola Tinubu wajen tabbatar da ganin cewa rashin kudi bai kawo tangarda ga karatun kowani dalibin Najeriya a manyan makarantu ba.

A cewarsa, an tanadi shirin ne saboda daliban Najeriya marasa karfi a manyan makarantu, kuma za a nemi rancen ne ta yanar gizo, rahoton Tori.ng.

ASUU tana adawa da tsarin rancen dalibai

A gefe guda, mun ji a baya cewa kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen jihar Bauchi, ta jaddada kudirinta na kin amincewa da ba dalibai rancen tare da neman a ba su tallafin karatu.

Jagoran kungiyar ASUU na shiyyar Bauchi, Farfesa Lazarus Maigoro ne ya bayyana haka a jiya a wajen bikin bayar da tallafin karatu ga dalibai marasa galihu 19 da ke shiyyar a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel