Dakarun Sojoji Sun Samu Galaba, Sun Halaka Ƴan Bindiga da Yawa a Jihohi 3 Na Arewa

Dakarun Sojoji Sun Samu Galaba, Sun Halaka Ƴan Bindiga da Yawa a Jihohi 3 Na Arewa

  • Sojojin Najeriya da wasu jami'an tsaro sun kashe ƴan bindiga 13 tare da kama mutane 271 da ake zargi a jihohi 3 na Arewa
  • Mataimakin kwamandan rundunar Operation Safe Haven, Terzungwe Iyua, ne ya bayyana haka a hedkwatar ƴan sanda da ke Jos ranar Jumu'a
  • Ya ce dakarun sun ceto mutane 79 da aka yi garkuwa da su tare da kwato muggan makamai sama da 100 da alburusai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jos, jihar Filato - Dakarun rundunar Operation Safe Haven, gamayyar jami'an hukumomin tsaro da ke kokarin tabbatar da zaman lafiya sun samu nasarar halaka ƴan bindiga 13.

Rundunar wadda aka ɗora wa alhakin wanzar da zaman lafiya a jihar Filato, da wasu sassan jihohin Kaduna da Bauchi, ta kuma kama wasu da ake zargi 271.

Kara karanta wannan

Rigima ta ƙara zafi a APC yayin da dakarun ƴan sanda suka ƙwace iko da sakateriya a jihar Arewa

Dakarun sojin Najeriya.
Sojoji Sun Kashe Yan Bindiga 13, Sun Kama Waɗanda Ake Zargi 271 a Filato, Bauchi da Kaduna Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

A cewar rundunar, jami'an tsaron sun samu wannan galaba ne a jihohin guda uku watau Filato, Kaduna da Bauchi, yankin da take yaƙi da ta'addanci da sauran miyagun laifuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin kwamishinan ƴan sandan Filato kuma mataimakin kwamandan rundunar Operation Safe Haven, Terzungwe Iyua, ne ya bayyana haka ga ƴan jarida jiya Jumu'a.

An ceto mutane daga hannun masu garkuwa

Da yake zantawa da manema labarai a Jos, Iyua ya ce jami'an tsaron sun samu wannan nasara ne tsakanin watan Janairu da Fabrairu, Daily Trust ta rahoto.

Ya ƙara da cewa bayan haka, sun kuma ceto mutane 79 da aka yi garkuwa da su daga hannun ƴan bindiga tare da ƙwato makamai da kayan aikin ƴan ta'adda.

Iyua ya yi bayanin cewa a cikin watanni biyu, "Mun kubutar da fararen hula 79 daga hannun masu garkuwa da mutane da kuma ‘yan fashi da makami.

Kara karanta wannan

DHQ: Dakarun Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta'adda Sama da 900, Sun Kama Wasu Masu Yawa a Najeriya

"Sannan dakaru sun kwato jimillar makamai daban-daban guda 110, sannan an kwato alburusai 1,161 daga hannun wadanda ake zargi da aikata miyagun laifuka.

Ya kuma yabawa al’ummar jihohin Filato, Kaduna da Bauchi bisa irin goyon baya da hadin kai da suke bayarwa wajen tabbatar da sahihan bayanai, Guardian ta tattaro.

Sojoji sun yi ɓarin wuta kan ƴan ta'adda

A wani rahoton kuma Jami'an rundunar sojin Najeriya sun yi nasarar halaka mayakan Boko Haram/ISWAP uku a yankin tafkin Chadi

Sojojin sun kuma kwato muggan makamai da kayan aikin ƴan ta'addan a samamen da ya ƙara nakasa su ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel