Innalillahi: An Tafka Babban Rashin Bayan Rasuwar Mataimakin Shugaban Masallacin Annabi (SAW)

Innalillahi: An Tafka Babban Rashin Bayan Rasuwar Mataimakin Shugaban Masallacin Annabi (SAW)

  • Al'ummar Musulmai sun shiga jimami bayan rasuwar mataimakin shugaban masallacin Annabi da ke birnin Madinah
  • Marigayin mai suna Sheikh Abdul Aziz bin Abdullah Al Falah ya rasu a yau Talata 20 ga watan Faburairu a Saudiyya
  • Hakan na cikin wata sanarwa da Masallacin mai daraja ya fitar a shafin X a yau Talata 20 ga watan Faburairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Madinah, Saudiyya - An shiga jimami yayin da mataimakin shugaban Masallacin Annabi Muhammad (SAW) ya rasu.

Marigayin Sheikh Abdul Aziz bin Abdullah Al Falah ya rasu a yau Talata 20 ga watan Faburairu a kasar Saudiyya.

An babban rashin mataimakin shugaban masallacin Annabi bayan ya rasu a yau
Marigayin ya rasu ne a yau Talata bayan fama da jinya. Hoto: @theholymosques.
Asali: Twitter

Wane matsayi marigayin ya rike kafin rasuwarsa?

Sheikh Abdul Aziz kafin rasuwarsa ya rike matsayin mataimakin shugaban Masallacin Manzon Allah (SAW) na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Sanatoci sun lalubo yadda Gwamnatin Buhari ta haddasa asarar Naira tiriliyan 17

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Masallacin mai daraja ya fitar a shafin X a yau Talata 20 ga watan Faburairu.

Sanarwar ta yi addu'ar Allah madaukakin sarki ya yi masa rahama ya sa Aljannar firdausi ce makomarsa.

Sanarwar ta ce:

"Sheikh Abdul Aziz bin Abdullah Al Falah, wanda ya rike mukamin mataimakin shugaban Masallacin Annabi da ke birnin Madina na lokaci mai tsawo ya rasu ne ranar Talata.
"Muna addu'ar ubangji ya gafarta masa kuma ya yafe masa."

Hadimin Masallacin Annabi ya rasu

Har ila yau, Allah ya yiwa daya daga cikinwadanda suka dade su na yi wa Masallacin Manzon Allah (SAW) hidima, Agha Habeeb Muhammad al-Afari, rasuwa.

Marigayin shine kuma ke kula da dakin da kabarin Annabi Muhammad yake inda ya shafe lokaci mai tsawo ya na wannan hidima ga dakin Allah.

Kara karanta wannan

El-Rufai @ 64: Abin da Shugaba Tinubu ya fada a kan tsohon Gwamnan Kaduna

Muhammad al-Afari ya rasu ne a ranar Laraba, 13 ga watan Yulin 2023, kamar yadda shafin Haramain Sharifain ya wallafa a shafin Twitter.

Sarkin Kuwait ya riga mu gidan gaskiya

A baya, kun ji cewa Sarkin Kuwait, Sheikh Nawaf Al-Ahmed Al-Sabah ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 86.

Marigayin ya rasu ne a yau Asabar 16 ga watan Disambar shekarar 2023 kamar yadda masarautar ta tabbatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel