An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Shahararren Jarumin Fina-Finai a Najeriya da Shekaru 81

An Shiga Jimami Bayan Rasuwar Shahararren Jarumin Fina-Finai a Najeriya da Shekaru 81

  • An shiga jimami bayan rasuwar shahararren jarumin fina-finan Nollywood, Jimi Solanke wanda ya riga mu gidan gaskiya
  • Marigayin ya rasu ne a yau Litinin 5 ga watan Faburairu bayan ya sha fama da jinya na tsawon lokaci
  • Dan Majalisar jihar da ke wakiltar Remo da Arewa, Hon. Dickson Awolaja ya tabbatar da mutuwar marigayin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun – Shahararren jarumin fina-finan Nollywood, Jimi Solanke ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 81 a duniya.

Marigayin ya rasu ne a yau Litinin 5 ga watan Faburairu bayan ya sha fama da jinya na tsawon lokaci.

Fitaccen jarumin fina-finai a Najeriya ya rasu
Fitaccen Jarumin Fina-Finai a Najeriya Ya Rasu. Hoto: Jimi Solanke.
Asali: Facebook

Yaushe marigayin ya rasu a jihar Ogun?

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban wata karamar hukuma a jihar ya yi murabus, bayanai sun fito

Channels TV ta tabbatar da cewa marigayin ya rasu yayin da aka dauke shi daga kauyensu a karamar hukumar Remo zuwa asibiti.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar da rasuwarshi a asibitin koyarwa na Jami’ar Babcock da ke Ilesan a jihar Ogun

Marigayin ya sha fama da jinya inda aka tabbatar ya yi ta kai kawo daga gida zuwa asibiti tun a watan Disambar 2023.

Dan Majalisar jihar da ke wakiltar Remo da Arewa, Hon. Dickson Awolaja ya tabbatar da mutuwar marigayin, kamar yadda TVC News ta tattaro.

Martanin dan Majalisa mai wakiltar yankin

Ya ce:

“Na samu labarin rasuwar dattijo Jimi Solanke dazu-dazu, tabbas mutuwarsa babban rashi ne ga Remo ta Arewa da jihar Ogun.
“Babban rashi ne ganin yadda ya ba da gudunmawa sosai ga ci gaban kasarmu baki daya, ubangiji ya yi masa rahama.”

Kara karanta wannan

Kogi: Yan bindiga sun sace fasinjojin wasu manyan motoci guda biyu a hanyar zuwa Abuja

Wannan rashi na zuwa ne kwana ɗaya bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar Yobe a jiya Lahadi 4 ga watan Faburairu a kasar Saudiyya.

An binne Bukar Abba a Saudiyya

Kun ji cewa bayan rasuwa tsohon gwamnan jihar Yobe, Bukar Abba Ibrahim an binne shi a kasar Saudiyya.

Marigayin ya rasu ne a jiya Lahadi 4 ga watan Faburairu bayan ya sha fama da jinya na tsawon lokaci.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi sallar jana’izarsa a masallacin Harami da ke Makka bayan idar da sallar Asuba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel