Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Gombe

Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Gombe

  • An shiga jimami bayan rasuwar Khalifan Darikar Tijjaniyya a Gombe, Sheikh Sheikh Muhammad Kobuwa a birnin Gombe
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin shehin malamin ya rasu ne a yau Juma'a 9 ga watan Faburairu a birnin Gombe
  • An tabbatar da cewa za a yi sallar jana'izarsa da misalin karfe 4:30 na yammacin yau Juma'a, a Idin Sarkin Gombe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - An wayi gari da mummunan labarin rasuwar Sheikh Sheikh Muhammad Kobuwa.

Marigayin shehin malamin ya rasu ne da safiyar yau Juma'a 9 ga watan Faburairu a birnin Gombe.

Shehin malamin addinin Musulunci ya riga mu gidan gaskiya a Gombe
Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Kobuwa Ya Rasu. Hoto: Sheikh Muhammad Kobuwa.
Asali: Facebook

Waye ne Sheikh Muhammad Kobuwa a Gombe?

Kara karanta wannan

Rundunar 'yan sanda ta bazama neman fitaccen malamin Musulunci ruwa a jallo, bayanai sun fito

Tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo ya sanar da rasuwar malamin a yau Juma'a 9 ga watan Faburairu a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin rasuwar marigayin shi ne Khalifan Darikar Tijjaniyya a Gombe wanda ya ba da gudunmawa sosai wurin yada koyarwar addinin Musulunci.

An tabbatar da cewa za a yi sallar jana'izarsa da misalin karfe 4:30 na yammacin yau Juma'a, a Idin Sarkin Gombe.

Martanin Sanata Ibrahim Dankwambo

Sanata Dankwambo ya nuna alhini kan rasuwar marigayin inda ya ce tabbas an samu wagegen gibi da zai yi wahalar cikewa.

Ya ce an yi babban rashi duba da salon karantarwarsa, jajircewa wajen faɗin gaskiya, hikima, tawali'u da kuma uwa uba horo da hadin kai.

Ya kara da cewa shehin malamin ya karar da rayuwarsa wajen karatu da karantar da addini, Zikiri da kuma Salati ga masoyinsa Manzon Allah (SAW).

Kara karanta wannan

Jimami yayin da fitacciyar jarumar fina-finai ta riga mu gidan gaskiya, an fadi abin da ya faru

A karshe, ya yi addu'ar Allah (SWT) yasa kyawawan halayensa su bi shi, Alkur'ani ya haska kabarinsa, masoyinsa Manzon Allah (SAW) ya karbi bakuncinsa.

Babban malamin Musulunci ya rasu a Gombe

A wani rahoton kun ji cewa Allah ya karbi rasuwar babban malamin addinin Musulunci a jihar Gombe.

Marigayin mai suna Sheikh Imam Sa'id Abubakar ya rasu bayan fama da jinya na tsawon lokaci.

Kafin rasuwarsa shi ne babban limamin masallacin Juma'a na Izala na biyu a jihar Gombe da ke Unguwar Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel