Ramadan: Gwamnan APC Ya Tausaya, Zai Raba Buhunan Shinkafa da Taliya Ga Talakawa a Watan Azumi

Ramadan: Gwamnan APC Ya Tausaya, Zai Raba Buhunan Shinkafa da Taliya Ga Talakawa a Watan Azumi

  • Gwamnatin Jigawa karkashin jagorancin Gwamna Umar Namadi ta fara shirin rabawa talakawan jihar kayan abinci saboda gabatowar Ramadan
  • Kwamishinan yaɗa labarai, Alhaji Sagir Musa, ya ce gwamnatin ta amince da siyo buhunan shinkafa 27,000 da katon-katon na taliya 10,8000 na tallafi
  • Ramadan shi ne wata na tara a kalandar Musulunci wanda mabiya addinin Musulunci ke yin ibadar azumi a kowace shekara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da siyan buhunan shinkafa 27,000 da katon-katon na taliyar spaghetti 10,800 domin rabawa talakawan jihar.

Gwamnatin karƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi Ɗan-Modi ta amince da siyo wannan kayan abinci ne domin rabawa jama'a saboda gabatowar watan azumin Ramadan.

Kara karanta wannan

Kamfanin Ajaokuta: Majalisa za ta binciki gwamnatin Yar'adua, Jonathan da Buhari kan fitar da $496m

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa.
Ramadan: Gwamnatin Jigawa Za Ta Raba Shinkafa da Taliya Ga Talakawa Hoto: Umar Namadi
Asali: Twitter

Kwamishinan yaɗa labarai, matasa, wasanni da al'adu na jihar Jigawa, Alhaji Sagir Musa ne ya bayyana haka ranar Laraba a Dutse, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wa za a rabawa tallafi a Jigawa?

Ya ce an amince da siyo buhunan shinkafa da taliyar ne a wurin taron majalisar zartarwa ta jiha (SEC) wanda ya gudana ranar Litinin, 26 ga watan Fabrairu, 2024, cewar tahoton The Cable.

A jawabinsa, kwamishinan yaɗa labaran ya ce:

"Majalisar zartarwa SEC ta aminta da kundin da ma'aikatar ayyuka na musamman ta gabatar na ba da kwangilar siyo kayan hatsi da za a rabawa al'umma.
"Za a raba wa mutane kayan abincin ne a matsayin tallafin da zasu tarbi watan azumin Ramadan na wannan shekarar 1445AH/2024.
"Majalisar ta amince da sayo buhunan shinkafa 27,000 da katan-katan na taliyar spaghetti 10,800 a matsayin tallafin rage raɗaɗi ga mazauna jihar."

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da al'ummar Musulmi a Najeriya da sauran ƙasashen duniya ke shirin fara azumun watan Ramadana wanda yake wajibi.

Watan Ramadan shi ne na tara a jerin watannin kalandar addinin musulunci kuma wata ne mai daraja wanda Allah SWT ke gafarta wa bayinsa.

Shin raba kayan abinci zai taimaki talaka?

Aminu Maje, mazaunin ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jigawa ya nuna farin cikinsa da wannan mataki da gwamnatin jihar ta ɗauka.

Matashin ya shaida wa Legit Hausa cewa akwai mutane da yawa da ke neman taimako kuma ga watan azumi na kara gabatowa.

Ya ce:

"Ai ba zaka gane ana cikin yunwa ba sai kana tare da mutane masu karamin karfi, yanzu waɗanda ke tashi da safe ba su da komai da zasu ci sune suka fi yawa.
"A ganina wannan yunƙuri ne mai kyau kuma dama muna yi wa gwamnatin Ɗanmodi fatan alheri, sai dai ba nan gizo ke saƙa ba, ya zama dole a sa ido tallafin ya kai ga mabuƙata."

Kara karanta wannan

Hukumar kwastam ta dakatar da sayar da kayan abinci kan farashi mai rahusa, ta faɗi dalili 1 tak

Shaibu na neman tada rikici a PDP

A wani rahoton na daban mataimakin Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya dira sakateriyar PDP ta ƙasa da ke Abuja ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu, 2024

Philip Shaibu ya buƙaci a ba shi satifiket na shaidar zama ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP a zaben jihar Edo mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel