Mummunan Hatsarin Mota Ya Salwantar Da Ran Amarya Da Wasu Mutum 12 a Arewa

Mummunan Hatsarin Mota Ya Salwantar Da Ran Amarya Da Wasu Mutum 12 a Arewa

  • An shiga jimami kan wani iftila'i da ya auku a jihar Neja sakamakon wani mummunan hatsarin mota
  • Mummunan hatsarin motan dai ya salwantar da ran wata amarya tare da ƙawayenta
  • Wasu daga cikin mutanen da hatsarin motan ya ritsa da su kuma sun samu munanan raunuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishɗi

Jihar Neja - Wani hatsarin mota da ya auku a kusa da Lukoro a cikin garin Edati na jihar Niger, ya yi sanadiyyar mutuwar wata amarya da wasu mata biyar, da ƙanin mijinta, da wasu mutum shida.

Hatsarin wanda ya auku sanadiyar wucewar ganganci, ya auku ne a yammacin ranar Juma’a lokacin da motar amaryar ta yi karo da wata.

Kara karanta wannan

Wani 'Bam' da ƴan ta'adda suka dasa ya tashi da mutane, ya tafka mummunar ɓarna a jihar arewa

Amarya ta rasu a hatsarin mota
Wata amarya ta rasa ranta a wani hatsarin mota a Neja Hoto: @FRSCNigeria
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta gano cewa mutum 20 ne suka yi hatsarin inda 13 daga ciki suka mutu sannan wasu bakwai suka samu munanan raunuka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Neja, Tsukwan Kumar, wanda ya tabbatar da faruwar hatsarin, ya ce hatsarin ya faru ne da wasu motoci guda biyu.

Yadda lamarin ya auku

Ya ce motocin sun haɗa da wata mota launin toka ƙirar Toyota Corolla wacce ta taho daga Mokwa zuwa Bida da wata motar bas ƙirar Nissan wacce ta nufi Minna daga Ogbomosho, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Ya ce waɗanda suka mutu sun haɗa da manyan mata takwas, manyan maza huɗu, da yaro namiji ɗaya yayin da manyan mata huɗu, babban namiji ɗaya, wasu ƙananan yara mace da namiji suka samu raunuka.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da amarya da ƙawayenta suka mutu jim kaɗan bayan ɗaura aure a arewa

Kumar ya ce an kai waɗanda suka jikkata zuwa cibiyar kula da lafiya ta tarayya (FMC) da ke Bida domin kula da lafiyarsu, yayin da tara daga cikin wadanda suka mutu aka miƙa gawarwakinsu ga ƴan uwansu daban-daban a wurin da hatsarin ya auku.

Ya ce sauran gawarwakin, kuma an kai su ɗakin ajiye gawa na babban asibitin Kutigi.

Mutum 16 Sun Rasu a Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa mutum 16 ne suka mutu yayin da wasu mutum huɗu suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a ƙaramar hukumar Makarfi da ke jihar Kaduna.

Hatsarin ya auku ne a kwanar Taban Sani, da ke Tashar Yari, kan hanyar Kano zuwa Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel