Mummunan Hatsari Ya Lakume Rayukan Akalla Mutum 6 a Babban Titin Kaduna Zuwa Zariya

Mummunan Hatsari Ya Lakume Rayukan Akalla Mutum 6 a Babban Titin Kaduna Zuwa Zariya

  • Wani mummuna hatsari ya rutsa da mutum 23 a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, inda mutum shida suka mutu, 11 suka jikkata
  • Hukumar kiyaye haddura ta kasa ta tabbatar da faruwar hatsarin a ranar Talata inda ta ce mota kirar Toyota ce ta afka wa wata mota
  • Kwamandan hukumar na Kaduna, Kabir Nadabo ya ce direbobin da ba ‘yan Kaduna ba ne ke haddasa yawancin hadarurruka a kan titin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) reshen jihar Kaduna, ta ce mutane shida ne suka mutu sannan 11 suka samu raunuka a wani hadarin mota da ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Tinubu ya dakatar da Halima Shehu watanni bayan nada ta a matsayin shugabar NSIPA

Kwamandan sashin, Mista Kabir Nadabo, ya shaida wa NAN a Kaduna cewa, hadarin motan ya afku ne a tashar Aliko da ke kan hanyar Kaduna zuwa Zariya a ranar Talata da misalin karfe 06:25 na safe.

Mutum shida sun mutu a mummunan hatsari kan hanyar Kaduna-Zariya
Hukumar FRSC ta ce mutum shida sun mutu sannan 11 sun samu raunuka a hadarin mota a hanyar Kaduna-Zariya. Hoto: @BashirAhmaad, @FRSCNigeria
Asali: Twitter

Nadabo ya ce, hatsarurrukan daban daban sun faru ne sakamakon gudun wuce sa a da kuma tukin ganganci, wanda hakan ya jawo dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na wani dan lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Direbobin da ke haddasa haddurra a titin Kaduna-Zariya

Sai dai ya ce tawagar masu aikin ceto na Zebra 35 Rigachikun sun kai dauki cikin gaggawa inda suka kai dauki, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Nadabo yace:

“Binciken farko da aka yi na hatsarin ya nuna cewa mutane 23 ne hatsarin ya rutsa da su; 11 sun jikkata, sai shida da suka rasa rayukansu."

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane sama da 100 a filato, majalisa ta nemi zama da jigogin tsaro

Ya ce bincike ya nuna cewa motar Toyota ta taho ne daga Ilesha, ta nufi Batsari, a jihar Katsina, wanda motar ta kwace masa saboda tsinanan gudun da ya ke yi, rahoton Tribune Online.

Nadabo ya ce direbobin da ba ‘yan jihar Kaduna ba ne ke haddasa yawancin hadarurrukan da ake yi a kan titin, kuma suna faruwa ne saboda gajiyar tuki ba hutawa.

Mutane da dama sun mutu a hatsarin mota kan hanyar Abuja-Kaduna

A wani labarin, wani hatsarin mota a kan titin hanyar Abuja zuwa Kaduna ya yi ajalin mutum hudu bayan motar da suke ciki ta yi karo da wata motar.

Mutum 59 ne suka jikkata a hatsarin motan wanda ya ritsa da akalla mutum 73 da ke cikin babbar motar daukar kayayyaki, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel