Tashin Hankali Yayin da Amarya da Ƙawayenta Suka Mutu Jim Kaɗan Bayan Ɗaura Aure a Arewa

Tashin Hankali Yayin da Amarya da Ƙawayenta Suka Mutu Jim Kaɗan Bayan Ɗaura Aure a Arewa

  • Wata sabuwar amarya da ƙawayenta sun rasu sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a jihar Neja
  • Ganau ya bayyana cewa motar amaryar ce ta kucce kana ta shiga Overtaking ba kan ƙa'ida ba, wanda ya sa motoci 2 suka yi taho mu gama
  • Kwamandan FRSC na jihar Neja ya ce tuni aka miƙa gawarwakin mamatan ga ƴan uwansu yayin da saurana aka aje a Asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Wata sabuwar amarya tare da ƙawayenta guda biyar sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su a yankin Lukoro, ƙaramar hukumar Edati a jihar Neja.

Ɗan uwan ango watau suruki ga amarya da ƙarin wasu mutane 6 na daga cikin waɗanda suka mutu a hatsarin wanda ya auku ranar Jumu'a da yamma.

Kara karanta wannan

Wani 'Bam' da ƴan ta'adda suka dasa ya tashi da mutane, ya tafka mummunar ɓarna a jihar arewa

Amarya ta rasu a hatsarin mota.
Amarya da Kawayenta Sun Mutu a Hatsarin Mota A Jihar Niger Hoto: FRSC
Asali: Facebook

Vanguard ta tattaro cewa motar da ta ɗauko amarya ta ƙawayenta ta kucce wa direban saboda tsananin gudu da tsere ba bisa ƙa'ida wanda ya sa ta yi taho mu gama da mota mai tahowa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganau ya ce mutum 20 ne mummunan hatsarin ya rutsa da su kuma daga cikinsu 13 sun rasa rayukansu yayin da sauran mutum bakwai ke kwance a asibiti cikin mawuyacin hali.

Rahoto ya nuna motar Bas ta haya kirar Nissan wadda ta yi taho mu gama da motar amaryan ta taso ne daga Minna da nufin zuwa Ogbomosho a jihar Oyo.

Wane mataki mahukunta suka ɗauka?

Da aka tuntubi babban kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) na jihar Neja, Tsukwan Kumar, ya tabbatar da faruwar lamarin.

A rahoton Premium Times, Kumar ya ce:

Kara karanta wannan

Gwamnan arewa ya cire tsoro, ya faɗi abu 1 da ƴan Najeriya zasu yi su samu sauƙi da ci gaba

“Hatsarin ya rutsa da motoci biyu, Toyota Corolla da ta ɗauko marigayiya amarya da sauransu daga Mokwa zuwa Bida da wata motar bas kirar Nissan ta haya wadda ta taso daga Minna zuwa Ogbomoso.
"Waɗanda suka mutu sun haɗa da ƴan mata 8, da maza matasa huɗu da yaro ɗaya yayin ƴan mata huɗu, matashi ɗaya da wasu kanana yara suka samu rauni."

Tuni dai aka miƙa gawarwakin ga ƴan uwansu bayan tattara bayanai yayin da ragowar huɗu da ba a gano bayanansu ba aka kai su asibitin garin Kutigi.

Ƴan bindiga sun sace babban mutum a Oyo

A wani rahoton kuma ƴan bindiga sun shiga har cikin gida, sun yi awon gaba da shugaban tashohin motoci na jihar Oyo, Alhaji Akeem Akintola.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun sace babban mutumin ne da sanyin safiyar yau Asabar, 27 ga watan Janairu, 2024.

Asali: Legit.ng

Online view pixel