Wani 'Bam' da Ƴan Ta'adda Suka Dasa Ya Tashi da Mutane, Ya Tafka Mummunar Ɓarna a Jihar Arewa

Wani 'Bam' da Ƴan Ta'adda Suka Dasa Ya Tashi da Mutane, Ya Tafka Mummunar Ɓarna a Jihar Arewa

  • Wani bam da ake zargin ƴan ta'adda ne suka dasa shi ya halaka manoma bakwai tare da jikkata wasu a jihar Borno
  • Zagazola Makama ya ce lamarin ya auku ne da safiyar ranar Litinin a titin Pulka/Firgi da ke ƙaramar hukumar Gwoza
  • A cewarsa, galabar da sojoji suka samu kan ƴan ta'addan ne ya sa suka koma amfani da bama-bamai kirar gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Wani abun fashewa da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne suka dasa shi ya halaka manoma bakwai a jihar Borno.

Lamarin dai ya afku ne yayin da ƴan ta'addan suka dasa bam ɗin a kan titin Pulka/Firgi da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar ta Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da amarya da ƙawayenta suka mutu jim kaɗan bayan ɗaura aure a arewa

Babban hafsan tsaron kasa, CDS Musa.
Abun Fashewar da Yan Ta'adda Suka Dasa Ya Halaka Manoma Bakwai a Jihar Borno Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

A cewar Zagazola Makama, wani kwararre kuma mai sharhi kan harkokin ƴan tada ƙayar baya a yankin tafkin Chadi, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Makama ya bayyana cewa bam ɗin ya tashi ne yayin da motar da manoman ke ciki ta taka shi ba tare da sanin tuggun da ƴan ta'ddan suka dasa ba.

Lamarin ya halaka mutane da dama

Ya kuma tattaro wata majiya na cewa fasinjojin motar guda bakwai ciki harda direba ne aka tabbatar sun mutu yayin da sauran mutum bakwai suka ji raunuka.

Rahoton da masanin ya wallafa a shafinsa na X wanda aka fi sani da Twitter ya nuna cewa ƴan ta'addan ISWAP da Boko Haram sun fara haka ne domin daƙile yunkurin sojojin Najeriya.

A ƴan watannin nan, dakarun sojoji na ci gaba da samun galaba kan ƴan ta'addan tare da kwace sansanin da suke ɓuya da kashe na kashewa, da lalata musu kayan aiki.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsarin mota ya salwantar da ran amarya da wasu mutum 12 a Arewa

Meyasa ƴan ta'adda suka koma dasa bam?

Makama ya kara da cewa 'yan tada kayar bayan sun fara amfani da bama-bamai a matsayin babbar dabarar yakinsu bayan da sojojin suka yi nasarar rage musu ƙarfi.

Ya ce mafi akasarin ababen fashewar da ƴan ta'addan ke amfani da su bama-bamai ne da aka kera a cikin gida.

A wani rahoton na daban Rundunar ƴan sanda ta samu nasarar ceto mutum 5 da aka yi garkuwa da su bayan musayar wuta da ƴan bindiga a Abuja.

Mai magana da yawun ƴan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta bayyana yadda aka yi gurmurzu kafin samun wannan nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel