Mummunan Hatsarin Mota Ya Salwantar da Rayukan Mutum 16 a Kaduna

Mummunan Hatsarin Mota Ya Salwantar da Rayukan Mutum 16 a Kaduna

  • An samu asarar rayukan mutum 16 bayan aukuwar wani mummunan hatsarin mota kan titin Kano zuwa Kaduna
  • Hatsarin motan wanda ya ritsa da wata motar bas ɗauke da mutum 20, ya kuma jawo mutum huɗu sun jikkata
  • Kwamandan hukumar FRSC wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce an aje gawarwakin waɗanda suka rasu a asibitin koyarwa na jami'ar ABU da ke Shika

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Mutum 16 ne suka mutu yayin da wasu mutum huɗu suka jikkata a wani hatsarin mota da ya auku a ƙaramar hukumar Makarfi da ke jihar Kaduna ranar Lahadi.

Hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11:20 na safe a kwanar Taban Sani, da ke Tashar Yari, kan hanyar Kano zuwa Kaduna, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

Abuja: Dakarun 'yan sanda sun ragargaji ƴan bindiga, sun ceto wani bawan Allah tare da kama 1

Hatsarin mota ya salwantar da rayukan mutum 16 a Kaduna
Rayukan mutum 16 sun salwanta a hatsarin mota a Kaduna Hoto: @FRSCNigeria
Asali: Facebook

Lamarin ya ritsa da wata motar bas da ta taso daga Kano kan hanyar zuwa Markudi a jihar Benue, rahoton PM News ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata sanarwa da kwamandan hukumar kiyaye haddura ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kaduna, Kabir Nadabo ya fitar, ya danganta hatsarin da gudu wanda ya wuce gona da iri, wanda ya sa motar ta ƙwacewa direban ta faɗa cikin rami.

Abin da bincike ya nuna kan hatsarin

Ya ce binciken farko da aka yi kan hatsarin ya nuna cewa mutum 20 ne hatsarin ya ritsa da su, inda mutum 16 suka mutu. Wasu mutum huɗu sun jikkata kuma an garzaya da su babban asibitin Makarfi domin kula da lafiyarsu.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Tawagar ceto ta RS1.111. a Tashar Yari ta mayar da martani cikin gaggawa tare da gudanar da aikin ceto. Binciken da aka yi kan hatsarin ya nuna cewa daga cikin mutum 20 da lamarin ya shafa, mutum huɗu sun jikkata, amma abin baƙin ciki, mutum 16 ne suka rasa rayukansu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da wani 'Bam' ya tashi da mutane a jihar arewa, ya tafka mummunar ɓarna

"An kai waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Makarfi domin yi musu magani cikin gaggawa yayin da aka aje gawarwakin waɗanda suka mutu a asibitin koyarwa na ABU da ke Shika a Zariya."

Mutum 10 Sun Rasu a Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani mummunan hatsarin mota ya salwantar da rayukan mutum 10 a jihar Kwara.

Hatsarin dai ya auku ne bayan wasu motoci guda biyu, babba da ƙarama sun yi taho mu gama a ƙaramar hukumar Moro ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel