An Sake Shigar da Fitaccen Jarumin Fina-Finai Dakin Tiyata Don Gutsere Masa Kafa, Ba Ya Iya Magana

An Sake Shigar da Fitaccen Jarumin Fina-Finai Dakin Tiyata Don Gutsere Masa Kafa, Ba Ya Iya Magana

  • An sake kwantar da John Okafor don sake gutsure wani sashi na kafarsa bayan yanke ta a watan da ta gabata
  • Jarumin wanda aka fi sani da Mista Ibu ya sha fama da jinya wanda ya yi sanadin gutsureta saboda nema masa lafiya
  • Shugaban kungiyar jaruman Najeriya, Emeka Rollas ya bayyana cewa za a sake yanke wani bangare na kafar da aka guntule a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, John Okafor ya sake shiga dakin tiyata don masa aiki a kafa.

Jarumin wanda aka fi sani Mista Ibu ya sha fama da ciwon kafa wanda sai da aka yanke masa a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa ya yi magana kan rade-radin ya yanke jiki ya fadi a bikin cika shekaru 61

Mista Ibu ya sake shiga dakin tiyata don karsa yanke wani bangare na kafarsa
An shigar da fitaccen jarumin fina-Finan Nollywood dakin tiyata don yanke kafarsa. Hoto: John Okafor.
Asali: Instagram

Tun yaushe jarumin ke fama da jinya?

Shugaban kungiyar jaruman Najeriya, Emeka Rollas ya bayyana cewa za a sake yanke wani bangare na kafar da aka guntule a watan da ta gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce dan wasan barkwancin ya sake shiga dakin tiyata don aiwatar da aikin a yau Asabar 16 ga watan Disamba, cewar Premium Times.

Rollas ya bayyana cewa a yanzu haka Mista Ibu ba ya iya ko yin magana a halin da ake ciki.

Ya kara da cewa hankalin jaruman Nollywood ya kara tashi musamman jinyar da jarumi Amaechi Muonagor ya ke yi na fiye da watanni biyu.

Amaechi dai na kwance ne a asibitin koyarwa na Jami’ar Nnamdi Azikwe da ke Nnewi a jihar Anambra.

Har ila yau, Rollas ya koka kan yadda rashin lafiyar jaruman ke kara munana ko wace rana, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana abu 1 tak da zai jawo wa Tinubu faduwa a 2027, ya ba da shawara

Yaushe aka yanke kafar jarumin?

Idan ba a manta ba, a ranar 6 ga watan Nuwamba ce iyalan Mista Ibu su ka sanar da cewa an yanke kafar jarumin saboda matsalar rashin lafiya.

Tun farko a watan Maris na shekarar 2022 aka kwantar da Mista Ibu a asibitin Zenith da ke Abuja inda ya ke zargin ‘yan kauyensu sun saka masa hannu ne.

Ya yi zargin cewa an yi kokarin saka masa gubar har sau biyu yayin da ya je shi kauyensu Nkanu ta Yamma da ke jihar Enugu.

An yanke kafar Mista Ibu a Abuja

A wani labarin, an yanke kafar jarumin fina-finan Nollywood, John OKafor saboda matsalar rashin lafiyar da ke damunsa.

Mista Ibu ya kwanta a asibitin Zenith ne tun a watan Maris na shekarar 2022 inda ya ke zargin an saka masa hannu daga kauyensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel