Ban taba son yarana su yi kama da ni ba domin ba ni da kyau: Jarumin fim ya magantu

Ban taba son yarana su yi kama da ni ba domin ba ni da kyau: Jarumin fim ya magantu

  • Shahararren jarumin fina-finan Najeriya, John Okafor wanda aka fi sani da Mista Ibu, ya bayyana cewa ba ya son 'ya'yansa su yi kama da shi
  • A cikin hirar da aka yi da shi kwanan nan, Mista Ibu ya yarda cewa ya yi addu'ar Allah ya sa yaransa su yi kama da mahaifiyarsu
  • Da yake bayanin dalilin addu’ar sa, mai wasan barkwancin ya lura cewa yana sane da cewa shi din ba kyakkyawa bane kuma baya son yaran sa su bi sahun sa

Fitaccen jarumin wasan kwaikwayo na Nollywood, John Okafor wanda aka fi sani da Mista Ibu, kwanan nan yayi magana ta gaskiya game da kamanninsa da kuma yadda baya son yaransa su bi sahun shi.

Da yake magana yayin wata hira da aka yi da shi kwanan nan a wani faifan bidiyo da Goldmyne TV ya sanya a shafin Instagram, tauraron fim din ya yarda cewa lokacin da ya haifi dansa na farko a 1991, ya roki Allah kan kada Ya sa jaririnsa ya yi kama da shi.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi ram da gurgu mai shekaru 22 kan zargin garkuwa da mutane

Ban taba son yarana su yi kama da ni a domin ba na da kyau: Jarumin fim ya magantu
Ban taba son yarana su yi kama da ni a domin ba na da kyau: Jarumin fim ya magantu Hoto: @mribu4real
Asali: Instagram

A cewarsa, ya kasance mai farin ciki da godiya ga Allah saboda haihuwar dansa amma yana son ya yi kama da mahaifiyarsa.

Da yake ci gaba da magana, Ibu ya lura cewa dalilin da ya sa yake addu’ar hakan shine saboda ya san cewa shi bai da kyau.

Jarumin wasan barkwanci ya ce koyaushe ya kasance mai fada ma kansa gaskiya kuma yana sane da kamannin sa kuma ba zai so wani daga cikin yaransa ya bi sahunsa ba ta wannan bangaren.

A cikin kalamansa:

"Ni mai fadawa kaina gaskiya ne, na san cewa ba ni da kyau, don haka ba na son wani daga cikin 'ya'yana ya bi ni a wannan ɓangaren."

Kalli bidiyon a kasa:

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun mayar da martani

Kara karanta wannan

Bawa: Abinda ya faru da ni bayan an gaggauta fitar da ni daga Aso Rock

Da yawa daga cikin masoyan taurarin fim din sun yi martani mai ban sha'awa game da fallasar Mista na cewa shi mummuna ne.

Karanta kaɗan daga cikin maganganun su a ƙasa:

Giddyboy007:

"Kai ne baka ga kyan ba."

Dcooldoll231:

"Ka yi gyara kawai ka ga yadda za ka yi kyau."

Adam Zango ya bayyana abu ɗaya da ya ke jira ya samu kafin ya dena yin fim kwata-kwata

A wani labarin, jarumin Kannyood, Adam Zango ya ce akwai yiwuwar ya dena yin fim a masana'antar fim na Hausa idan ya samu wata sabuwar hanyar samun kudaden shiga.

Jarumin ya ce a sha'awar da ya ke yi wa masana'antar na fim ta ragu duk da cewa har yanzu yana cikinta. Ya ce idan ya samu hanyar samun kudaden shiga da ta fi fim, zai dena yin fim.

A cikin hirar da aka yi da shi a BBC Hausa a ranar Asabar, Zango ya ce:

Kara karanta wannan

Aisha Yesufu ta fada murna, dan ta ya kammala digiri a jami'ar Ingila

"Ni fitaccen jarumi ne a Kannywood kuma ina yi wa Allah godiya bisa wannan baiwar, amma duk da haka ina da shirin neman wata hanyar samun kudi da ta fi wannan, zan dena fim din inyi wani abu daban da zarar na samu."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng