Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Magana Kan Rade-radin Ya Yanke Jiki Ya Fadi a Bikin Cika Shekaru 61

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Magana Kan Rade-radin Ya Yanke Jiki Ya Fadi a Bikin Cika Shekaru 61

  • Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya bayyana cewa yana da zazzabin cizon sauro da ya hade masa da gajiya
  • Akpabio, wanda ya ce ya gaji sosai, ya shawarci jama'a da su dunga shan ruwa a kullun domin kada su galabaita
  • Ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga rade-radin cewa ya yanke jiki ya fadi a otel din Transcorp Hilton da ke Abuja sannan an kwashe shi zuwa asibiti

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya magantu kan rade-radin cewa ya yanke jiki ya fadi awajen bikin cikarsa shekaru 61 a Abuja a ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba.

Akpabio ya ce ya kamu da cutar zazzabin cizon sauro, wanda ya kara tabarbarewa sakamakon gajiyar da ya yi, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

"Ainahin dalilin da yasa muka tsige gwamna da yan majalisar PDP 16": Alkalin kotun daukaka kara

Akpabio ya ce zazzabin cizon sauro ke damunsa
Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Magana Kan Rade-radin Ya Yanke Jiki Ya Fadi a Bikin Cika Shekaru 61 Hoto: Nigeria Senate
Asali: Facebook

Ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a majalisar dattawa a ranar Juma’a, 15 ga watan Disamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma duk bayaninsa shugaban majalisar dattawan bai ce uffan ba kan ko ya fadi ko kuma bai fadin ba, jaridar Premium Times ta rahoto.

“Abin da ya faru bayan taron abu ne irin na dan adam. Na je gida sannan na kira likitocina sannan aka tabbatar min da cewa na kamu da zazzabin cizon sauro, wanda ya hade da gajiya, wanda za a kuma iya bayyana shi ta wata hanyar galabaita.
“A zahirin gaskiya, kowa zai iya gajiya. Don Allah, ku dunga shan ruwa kullum don kada ku galabaita.”

Akpabio ya yanke jiki ya fadi

A baya mun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godwill Akpabio ya fadi yayin da ake bikin zagayowar ranar haihuwarsa a Abuja. Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 14 ga watan Disamba yayin bikin cika shekaru 61 na shugaban Majalisar, Punch ta tattaro.

Kara karanta wannan

Idan aka halatta shigo da shinkafa, siminti da sauransu, farashinsu zai sauko – Bankin duniya

Bikin shi ne karo na biyu da aka gudanar tun bayan fara bikin a ranar 9 ga watan Disamba a birnin Uyo da ke jihar Akwa Ibom.

Sai dai kuma, kakakin Majalisar, Yemi Adaramodu ya musanta faruwar lamarin bayan wakilin Punch ya tuntube shi kan abin da ya faru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel