Likitoci Sun Yanke Wa Jarumin Fina-Finan Najeriya Kafa Don Ceto Ransa

Likitoci Sun Yanke Wa Jarumin Fina-Finan Najeriya Kafa Don Ceto Ransa

  • Likitoci sun yanke kafar shahararren jarumin fina-finai na Kudancin Najeriya, John Okafor, wanda aka fi sani da Mr Ibu, a wani yunkuri na ceto rayuwarsa
  • Tun a watan Oktoba Mr Ibu da iyalansa suka nemi taimakon al'umma kan irin halin da ya ke ciki na rashin lafiya, wanda a karshe ya yi sanadiyar rasa kafar ta sa
  • Okafor, wanda ya yi fice a fina-finan barkwanci, ya yi shuhura ne tun bayan da ya fito a wani fim mai suna 'Mr Ibu in London' inda lakanin Mr Ibu ya bi shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A cikin wata sanarwa daga iyalan shahararren jarumin barkwanci John Okafor, da aka fi sani da Mr Ibu, sun bayyana cewa likitoci sun yanke daya daga cikin kafafuwan jarumin domin ceto ransa.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan Boko Haram sun sake yi wa manoma 9 yankan rago a Borno

Labarai a watan Oktoba sun bayyana yadda jarumin fina-finan ya kamu da cuta, inda har ta kai shi ga neman taimakon kudaden da zai yi jinyar rashin lafiyarsa.

Mr Ibu
Likitoci sun yi nasarar yanke wa jarumin fina-finan Najeriya kafa don ceto sansa Hoto: RealMrIbu
Asali: Instagram

A cikin sanarwar da aka wallafa a shafin jarumin na Instagram, an bayyana cewa an yi wa jarumin aiki cikin nasara, inda aka yanke kafarsa a kokarin likitocin na ceto ransa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

Barkanku 'yan Nijeriya. Muna son yin amfani da wannan damar wajen godewa dukkan wadanda suka taimaka wa mahaifinmu; cewa mun gode ba zai wadatar ba, Allah ne kadai zai iya saka maku da irin taimakon da ku ka yi mana.
Misalin karfe 1 na ranar yau, an shigar da mahaifinmu dakin tiyata, inda aka yi masa aiki har sau bakwai, domin ceto ransa tare da kara masa karsashin warkewa da wuri, akan hakan ne aka yanke masa kafa daya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da walkiya ta kashe dalibai suna tsaka da buga kwalla a Anambra

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

Wannan matakin na yanke masa kafa ya jefa mu cikin mawuyacin hali, amma dole mu karbi sabuwar kaddarar rayuwar da mahaifinmu zai fuskanta, hakan ne kawai zai sa ya ci gaba da rayuwa.
Sai dai har yanzu, muna ci gaba da neman taimako daga 'yan Najeriya, domin a wannan gabar, mahaifinmu yana bukatar duk wani taimako da zai iya samu."

A karshe iyalan jarumin sun yi godiya ga daukacin al'umar da suka taimaka su, tare da fatan jarumin zai yi wa al'umma godiya da kansa da zaran ya samu saukin yin hakan.

Bukola Saraki ya dauki nauyin asibitin Mr Ibu

A wani labarin makamancin wannan, gidauniyar Abubakar Bukola Saraki ta biya dukkanin kudaden asibitin shahararren jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu, jaridar Legit Hausa ta ruwaito.

An bayyana wannan labarin ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a shafin gidauniyar na Facebook a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.