Bola Tinubu da Kashim Shettima Za Su Kashe Naira Biliyan 15 a Tafiye Tafiye a Shekara 1

Bola Tinubu da Kashim Shettima Za Su Kashe Naira Biliyan 15 a Tafiye Tafiye a Shekara 1

  • Fadar shugaban kasa ta samu kason biliyoyi daga cikin kasafin kudin shekarar 2024 da gwamnatin tarayya ta yi
  • Abin da aka ware da sunan tafiye-tafiyen Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a shekarar badi ya zarce N15bn
  • Shugabannin Najeriya za su iya batar da sama da N600m kan kayan abinci, sannan za a saye motocin N6bn a 2024

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima da hadimansa za su kashe N15.961bn a wajen tafiye-tafiye a shekara mai zuwa.

Vanguard ta ce an samu wadannan bayanai ne daga kasafin kudin da Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya gabatar gaban majalisar tarayya.

Bola Tinubu da Kashim Shettima
Bola Tinubu da kasafin kudin 2024 Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Yawon Tinubu, Shettima zai ci N16bn

Kara karanta wannan

Tinubu ya warewa Buhari, Osinbajo da Jonathan naira biliyan 13 a kasafin 2024

Bola Ahmed Tinubu da mukarrabansa za su batar da N7.630bn da sunan tafiye-tafiye a cikin gida da zuwa kasashen ketare a shekarar badi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan 'yan majalisa sun amince da kasafin kudin yadda aka gabatar da shi, mataimakin shugaban kasa zai ci N6.902bn a zirga-zirga.

Kasafin kudin na 2024 ya nuna tafiye-tafiyen da shugaban kasan da mataimakinsa za su yi a cikin Najeriya za su lashe N638.5m da N618.39m.

An ware wasu N6.484bn saboda tafiye-tafiyen jami’an da ke cikin fadar Aso Rock yayin da aka samu rahoto har dabbobi za su samu N201m.

A shekara mai zuwa, The Nation ta ce fadar shugaban kasa za ta kashe N40.61bn wajen ayyuka da biyan albashin ma’aikata da sauransu.

Gina ofisoshi da gyare-gyare a Aso Rock

Gyare-gyaren wuta da sauran abubuwa da za ayi za su ci N9bn a fadar shugaban kasar, wani fitaccen kamfanin kasar waje ake ba aikin.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba na Kano zai faranta ran tsofaffin ma’aikata, an tsaida ranar fara biyan kudin giratuti

Abin da aka ware domin gina ofisoshin masu ba shugaban kasa da mataimakinsa shawara shi ne N3bn a lokacin da ake kukan rashin kudi.

Za kuma a kashe wasu N3bn a saye da gyaran kayan aikin fadar shugaban kasa.

Motoci da abincin Tinubu za su ci N11bn

Motoci kurum za su ci N6bn a fadar shugaban kasa kamar yadda aka yi lissafin cewa Tinubu da mataimakinsa za su ci abinci na N5.128bn.

A cikin wannan N5.128bn, za a biya kudin taro da shakatawa da sayen manhajojin komfuta, gyare-gyaren komfutocin za su ci N980m.

Tinubu ya dawo da kwangilar INTEL

Da aka soke kwangilar da aka ba INTEL, an samu labari cewa hakan ya jawo asarar N120bn a cikin 'yan shekaru ga gwamnatin tarayya.

Da gwamnati ta ji uwar-bari, an kira kamfanin ya cigaba da aiki a tasoshin ruwan Najeriya bayan Atiku Abubakar ya saida hannun jarinsa.

Kara karanta wannan

N27.5tr: Majalisar wakilan tarayya da Sanatoci sun fara tafka mahawar kan kudirin kasafin kuɗin 2024

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng