An Sanar da Lokacin da Tinubu Zai Gabatar da Kasafin Kudin 2024 a Majalisar Tarayya

An Sanar da Lokacin da Tinubu Zai Gabatar da Kasafin Kudin 2024 a Majalisar Tarayya

  • Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da kundin kasafin kudi a gaban Sanatoci nan da wasu ‘yan kwanaki a zauren majalisa
  • Sanata Solomon Adeola ya ce shirye-shirye ya kankama domin karbar takardar tsarin kudin da za a kashe na MTEF-FSP
  • ‘Dan majalisar ya nuna za su yi bakin kokarinsu ta yadda talaka zai amfana da kasafin kudin shekarar ta 2024 mai zuwa

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta fara shirye-shiryen kasafin kudin farko da Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai gabatar a mulkinsa.

Kafin karshen Nuwamba, rahoton Premium Times ya tabbatar da cewa za a gabatar da kasafin kudin da Najeriya za ta kashe a 2024.

Shugaban kwamitin kasafi a majalisar dattawa, Solomon Adeola ya shaidawa ‘yan jarida wannan wajen rantsar da kwamitinsu jiya.

Kara karanta wannan

Za a Binciki N11.3tr da Buhari da Jonathan su ka kashe a Matatu Daga 2010-2023

Bola Tinubu
Za a gabatar da kasafin kudi Hoto: Asiwaju Bola Tinubu
Asali: Facebook

An kafa kwamitin kasafin kudi a Majalisa

Sanata Solomon Adeola ya yi magana da manema labarai a taron farko da kwamitin ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

‘Dan majalisar na Ogun ta yamma ya kuma tabbatar da cewa a makon gobe Bola Tinubu zai gabatar masu da tsarin tattali (MTEF-FSP)

"Za mu yi aiki da kyau a kasafin kudin. Aikinmu shi ne mu tabbatar da kasafin ya biya bukatar mutanemmu. Za mu duba shi da kyau.
Mu na sa ran MTEF a makon gobe kuma da zarar mun karbi takardar, kwamitin tattalin arziki zai karba domin ya fara yin aiki a kan shi."

- Solomon Adeola

Ministan kudi da tattalin arziki da ministan tsare-tsare da kasafi su na ta aiki dare da rana.

Babu cushe a kasafin kudin 2024

Leadership a rahoton da ta fitar, ta ce Adeola ya yi alkawarin gwamnati za tayi kokarin ganin kasafi na aiki daga Junairu zuwa Disamba.

Kara karanta wannan

Hanya 1 Za a Bi Domin Hana Farashin Dala Tashi - Tsohon Mataimakin Sanusi a CBN

Sanatan ya kara da cewa majalisar tarayya ba za ta yi cushe a kundin kasafin ba kamar yadda aka taba zargin an yi a shekarun baya.

Aikin bangaren zartarwa ne yin kasafi da aiwatar da shi, Sanatan na APC ya ce na su shi ne dubawa da sa ido yayin da ake shirin kashe N26tr.

Majalisa za ta binciki gwamnati

An ji labari N11, 349, 583, 186, 313.40 aka batar domin matatun kasar nan su iya tace danyen mai daga zamanin Ummaru ‘Yar’adua zuwa yau.

Bayan nan gwamnatin tarayya ta kashe $592, 976, 050.00, €4, 877, 068.47 da £3, 455, 656.93, majalisar tarayya ta ce dole a binciki wannan batu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel