Matashiyar Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Wuff Da Angonta Dan Koriya, Ya Taka Rawan Yarbawa a Bidiyo

Matashiyar Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Wuff Da Angonta Dan Koriya, Ya Taka Rawan Yarbawa a Bidiyo

  • Wani ango dan Koriya ya tashi kan mutane a soshiyal midiya yayin da ya taka rawan wakar Yarbawa a ranar aurensa
  • Mutumin ya nuna bajinta yayin da yake bibiyar wakar inda yake sanye da saki dinkin babbar riga da hula
  • Yan TikTok da dama sun ce rawansa ya sanya su murmushi, kuma cewa lallai ya shafe kwanaki yana bita

Wani mutumin kasar Koriya da ya auri Bayarabiya ya kayatar da mutane da dama a ranar aurensa yayin da ya yi shigowar kasaita tare da yan uwa da abokansa.

Gaba daya abokan angon sun sanya babbar riga yayin da suke rawan wakar Yarbawa ta Asake Omo Ope.

Dan Koriya ya yi wuff da Bayarabiya
Matashiyar Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Wuff Da Angonta Dan Koriya, Ya Taka Rawan Yarbawa a Bidiyo Hoto: @teamdfams
Asali: TikTok

Ango dan Koriya ya tashi kan jama'a a wajen aurensa

Angon ya kasance cikin farin ciki tsatsa yayin da yake kada hannaye da kafafuwansa.

Kara karanta wannan

“Ba a Jin Kanmu”: Kawaye Biyu Na Soyayya Da Saurayi Daya, Sun Yi Sharholiya Da Shi a Bidiyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da suka ga yadda angon ke kokarin rawa sai kace dan Najeriya sun ce lallai ya shafe tsawon kwanaki yana bita don burgewa.

Ya rera wasu baitukan wakar yayin da sauti ya karade dakin taron. Ya kasance cike da kuzari da kwalisa yayin da ake masa yayyafin dala.

Shafin @teamdfams ne ya yada bidiyon nasa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

OLA ya ce:

"Allah kadai ya san kwana nawa ya kwashe yana bita kafin ranar auren."

Your girlfriend ta ce:

"Awwwnn wacece ta auri lee min hoo."

maryanneyusuf ta ce:

"Shin ni kadai ce nake murmushi yayin kallon wannan."

osasonayemi ya ce:

"Barka da zuwa gida Adebowale."

Sophie_face_’n’_spa ta ce:

"Kaina yana ta tashi. Ina taya wannan matar da aka yi aurenta murna."

Michellentee ta ce:

Kara karanta wannan

“Ba Ki Da Hankali Ne?” Wani Mutum Ya Kurma Ihu Bayan Ya Kama Mai Aiki Tana Wanke Masa Kayan Wuta Da Sabulu

"Don Allah ku dunga karin bayani ina bukatar miji dan Koriya nima."

Reineer Velasquez ta ce:

"Surankan da ke baya sun ga kudi."

Actress Diamond1 ta ce:

"Kun fara kuma wacece ta je ta auri wanda nake mutuwar so."

“Ba Ma Fada”: Kawaye biyu da ke soyayya da saurayi daya sun yada bidiyonsu

A wani labarin kuma, mun ji cewa Yan Najeriya sun yi martani a kan wani bidiyo da ke nuna wani mutum da ke soyayya da kawaye biyu a lokaci guda.

Wani shafin Instagram, @naijaeverything, ya yada bidiyon a dandalin soshiyal midiya, inda ya kara da cewar yan matan ba sa fada da junansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel