Yadda Sojojin Amurka ke Aiki da Najeriya gabanin Zaben 2027

Yadda Sojojin Amurka ke Aiki da Najeriya gabanin Zaben 2027

  • Sojojin Najeriya na samun bayanan sirri da hotunan tauraron dan adam daga Amurka domin kai hare-hare kan shugabannin ’yan ta’adda
  • Ministan Tsaro ya ce sojoji sun kashe wasu shugabannin ’yan bindiga da ’yan ta’adda a hare-hare da suka kai a yankunan Arewa
  • Gwamnati na kuma amfani da bayanan sirri wajen karfafa tsaro gabanin zaben shugaban kasa na watan Janairun 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FFCT, Abuja – Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa sojojin kasar na samun tallafin bayanan sirri da hotunan tauraron dan adam daga Amurka domin fatattakar ’yan ta’adda da shugabannin ’yan bindiga.

Musa ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, inda ya ce hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka na taimakawa sojoji wajen gano maboyar ’yan ta’adda da kai musu hare-hare cikin sauri.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tausaya wa matasan da aka kama kan jifan motocinsa a masallacin Juma'a

Christopher Musa
Ministan tsaro, Christopher Musa. Hoto: General CG Musa
Source: Twitter

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ministan ya ce an kashe wasu shugabannin ’yan bindiga da ’yan ta’adda a hare-haren da sojoji suka kai cikin dare a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

Amurka na taimakon Najeriya

Janar Musa ya ce bayanan sirri, hotunan tauraron dan adam da horon da Amurka ke bai wa sojojin Najeriya sun inganta karfinsu wajen gano inda ’yan ta’adda suke da kuma kai musu hare-hare.

Ya ce Najeriya da Washington na ci gaba da fadada hadin gwiwarsu ta fuskar tsaro yayin da kasar ke fama da hare-haren ’yan ta’addan Boko Haram da ISWAP a Arewa maso Gabas, ’yan bindiga a Arewa maso Yamma da masu garkuwa.

Ministan ya kuma bayyana cewa Najeriya na sa ran samun karin jiragen yakin sama masu saukar ungulu daga Amurka da Italiya, bayan kaddamar da wasu jiragen da aka samu a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Tinubu ya amince a dauki sababbin sojoji 28000 da ‘yan sanda 50000 aiki

A watan Mayun 2026, sojojin Najeriya da Amurka sun kashe Abu-Bilal al-Minuki, wanda Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a matsayin na biyu mafi girma a shugabancin kungiyar ISIS a duniya.

Ana karfafa tsaro gabanin 2027

TRT ta wallafa cewa Musa ya ce hukumomin tsaro na kara shirin tunkarar zaben watan Janairun 2027, inda Shugaba Bola Tinubu ke neman zarcewa kan mulki na wa’adi na biyu.

Ya bayyana cewa ana amfani da bayanan sirri wajen gudanar da hare-hare domin dakile duk wani yunkurin tayar da hankali kafin zabe, yayin gudanar da shi da kuma bayan kammala kada kuri’a.

Ministan ya ce hukumomin tsaro na sa ido kan yadda kungiyoyin ’yan ta’adda ke amfani da fasahar Starlink, kudi ta intanet da jiragen sama marasa matuka wajen gudanar da ayyukansu.

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka na shirin shiga jirgi zai yi tafiya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya kara da cewa Najeriya na aiki tare da hukumomin Amurka domin dakile hanyoyin samun kudin da kungiyoyin ke amfani da su wajen daukar nauyin ayyukansu.

Tinubu ya kawo tsarin tsaro

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da wani shirin dabarun ayyukan tsaro na tsawon shekara biyar domin karfafa tsarin tsaron Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fitar da sabon tsarin tsaro da zai kawo zaman lafiya a shekara 5

Rahoto ya nuna cewa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa ta jam’iyyar APC ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi.

Sanarwar ta bayyana cewa daya daga cikin abubuwan da shirin ya kunsa shi ne daukar karin jami’an tsaro 78,000, wadanda za su hada da sojoji da ’yan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng