Kamar a Fim: Hadadden Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Budurwa Ta Auri Dan Koriya, Mata Sun Mato a Kansa

Kamar a Fim: Hadadden Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Budurwa Ta Auri Dan Koriya, Mata Sun Mato a Kansa

  • Wani hadadden bikin aure da aka kulla tsakanin wani mutumin kasar Koriya da sahibarsa yar Afrika ya yadu a soshiyal midiya
  • Hotuna da bidiyon auren da aka yi a gargajiyance ya burge mutane da dama, musamman mata da suka mato kan mijin
  • Kyakkyawar amaryar ta kasance tare da mahaifiya, kanwa da kawayenta a bikin al'adan na kasar Koriya

Wata matashiyar budurwa yar Afrika ta burge zukata yayin da ta wallafa hotuna da bidiyon shagalin aurenta da wani dan kasar Koriya.

Faith, wacce ba a san daga wani yanki na Afrika ta fito ba, ta matukar haduwa a cikin kaya irin na mutanen kasar Koriya yayin da ta fito tare da hadadden mijinta.

Daurin auren yar Afrika da dan Koriya
Kamar a Fim: Hadadden Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Budurwa Ta Auri Dan Koriya, Mata Sun Mato a Kansa Hoto: @faith.oooh
Asali: TikTok

Bikin al'adarsu ya samu halartan masu fatan alkhairi da masoya daga bangarorin biyu. A bangaren kyakkyawar amaryar, mahaifiyarta, kanwarta da kawayenta sun hallara.

Kara karanta wannan

Allah Daya Gari Banban: Yadda Aka Sha Shagalin Bikin Wani Basarake Da Amaryarsa Kada

Masu amfani da soshiyal midiya sun mato a kan hotunan ma'auratan wadanda sukafito daga nahiya daban-daban haka ma masoyansu. Musamman yan mata suka dunga mamakin yadda amaryar ta ji yin irin rayuwar da take mafarki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba a bar masoya kallon fina-finan K-Drama na kasar Koriya a baya ba yayin da duk suka mato a kan ma'auratan.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Royalty ta ce:

"Yaya kika ji yin irin rayuwar da kike mafar ...mu yan matan Afrika da muka mato kan kallon wasannin kdrama."

user5085313420797 ta ce:

"Kawai ina duddubawa kasa sai hadadden bidiyon ya ja hankalina, Allah ya albarkace ki yar'uwa."

kamobello ta ce:

"Shin TikTok na karanta zukata ne? Na dade ina kallon fina-finan K-dramas kuma na dade ina burin auren dan Koriya."

Marvel_da_black ta ce:

Kara karanta wannan

Yadda Yan Daba Suka Caccaki Wani Dan Kasuwa Har Lahra a Jihar Kano

"A madadin yan matan Najeriya, ya ake ji idan mutum ya tsinci kansa a rayuwar Koriya da yake mafarki."

Just Chula ta ce:

"Ya yi kama da wasan kwaikwayo."

Nomsa Khanyile ta ce:

"Abun da Allah ya hada mutum bai isa ya raba ba...Allah ya kara albarka a aurenku."

Basarake ya angwance da kada a kasar Mexico

A wani labarin kuma, mun ji cewa basaraken wani karamin kauye a kasar Mexico ya auri wata kada.

An yi wa kadar ado da kaya irin na amare yayin da aka daure bakinta don kudin kada ta kai farmaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel