Yadda Matashi Ya Nemi Auren Wata Dattijuwar Baturiya Cikin Salo, Bidiyon Ya Yadu

Yadda Matashi Ya Nemi Auren Wata Dattijuwar Baturiya Cikin Salo, Bidiyon Ya Yadu

  • An gano wani mutum a wani bidiyo da ya yadu yana sanyawa wata baturiya da ke zaune a gado zobe
  • A cikin bidiyon wanda tuni ya yadu, mutumin ya nemi dattijuwar matar ta aure shi, yana mai nuni ga irin son da suke yi wa junansu
  • Bayan dogon nazari, sai matar ta amsa tayinsa sannan ta mika masa hannu don ya sanya mata zoben alkawari

Wani bidiyo ya nuno lokacin da wani mutum ya sanyawa sahibarsa zoben alkawari sannan ya nemi ta amince ya yi wuff da ita.

Bidiyon da ke nuna lokacin da ya nemi aurenta ya dauka hankalin mutane da dama a soshiyal midiya, inda suka garzaya sashin sharhi domin tofa albarkacin bakunansu.

Matashi ya nemi auren dattijuwar baturiya
Yadda Matashi Ya Nemi Auren Wata Dattijuwar Baturiya Cikin Salo, Bidiyon Ya Yadu Hoto: Twitter/@Aqualady6666.
Asali: Twitter

A bidiyon wanda Aqualady ta yada, an gano mutumin da sahibarsa a cikin wani daki inda ya fito da zoben alkawari.

Kara karanta wannan

Wata Uwa Ta Fashe Da Dariya Ba Kakkautawa Bayan Ganin Saurayin Diyarta a Karo Na Farko, Faifan Muryar Ya Yadu

Mutumin ya sanar da matar cewa yana burin kasancewa tare da ita iya tsawon rayuwarsa sannan ya bukaci ta amshi zoben daga gare shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashi ya nemi auren baturiya

Akwai wata mata a cikin dakin wacce ta bukaci dattijuwar baturiyar da ta amsa tayin matashin, kuma sai ta aikata hakan.

Ta mika masa hannunta sannan ta karbi zoben, lamarin da ya haifar da farin ciki da murna a cikin dakin.

Mutane sun lura cewa baturiyar dattijuwa ce, kuma nan take suka fara kwararo zantuka a sashin sharhi na bidiyon. Sai dai wasu sun bukaci magauta su yi shiru da bakinsu sannan su kyale masoyan su yi harkokinsu cikin jin dadi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Goble_services ta ce:

"Lol. Matashi na zuba jari ta hanyar neman aure. Mutane da dama za su aikata haka idan suka samu dama."

Kara karanta wannan

“Allah Ya Sauke Ki Lafiya”: Bidiyon Wata Wada Dauke Da Tsohon Ciki Ya Yadu

@Djkayceebeat ta ce:

"Shin zai aikata hakan da babu kudi? Akwai tarin riba a karshe."

@naati_bryhms ta ce:

"Ko a jikinta ma."

@okt_ranking33 ta ce:

"Soyayya da dadi fa."

Dan Najeriya ya kama yaron da ke wanke masa mota a boye

A wani labarin, wani dan Najeriya ya nunawa duniya wani matashin yaro da ke wanke masa motarsa ba tare da saninsa ba.

Mutumin mai suna @koffiseed a TikTok, ya yada bidiyon da ya dauki yaron mai suna Neche cikin sirri a wannan rana, inda ya nemi shawarar mutane kan tukwicin da ya kamata ya ba shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel