Yadda 'Yan Adawa ke Kara Kokarin Haduwa Su Kifar da Tinubu a 2027
- ’Yan adawa a Najeriya na ci gaba da tattaunawa kan samar da dan takara guda daya da zai kalubalanci APC a zaben shugaban kasa na 2027
- Atiku Abubakar, Peter Obi, Seyi Makinde da sauran ’yan takarar jam’iyyun adawa na cikin wadanda ke tattaunawar, amma har yanzu ba a cimma matsaya ba
- Taron da za a gudanar a Abuja ranar 23 ga Nuwamba na iya zama wani muhimmin mataki wajen tabbatar da ko za su iya hada kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Yunkurin da jam’iyyun adawa ke yi na hada kai domin tsayar da dan takara guda daya a zaben shugaban kasa na 2027 na ci gaba, duk da cewa har yanzu ba su cimma matsaya kan wanda zai wakilce su ba.

Kara karanta wannan
"Yadda Pater Obi da Kwankwaso za su kifar da Tinubu a zaben 2027 da taimakon Allah"
Tattaunawar ta hada da manyan ’yan takarar shugaban kasa daga jam’iyyun adawa, ciki har da Atiku Abubakar na jam’iyyar ADC, Peter Obi na NDC, Seyi Makinde na APM, Donald Duke na PRP da Adewole Adebayo na SDP.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana sa ran taron da hadakar Coalition for Democracy za ta shirya a Abuja ranar 23 ga Nuwamba zai zama wani muhimmin mataki wajen tattauna makomar hadin kan jam’iyyun.
Atiku, Obi da Makinde na tattaunawa
Gwamnan jihar Oyo kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APM, Seyi Makinde, ya tabbatar da cewa yana tattaunawa da Atiku Abubakar da Peter Obi kan yiwuwar hada kai gabanin zaben 2027.
Makinde ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Arise News ta watsa ranar Juma’a, inda ya ce tattaunawar na gudana sosai.
Ya ce babban burin tattaunawar shi ne samar da kyakkyawan shugabanci da kuma kawo karshen mulkin APC a matakin tarayya.
Sai dai gwamnan ya jaddada cewa hadin kai ba yana nufin dole ne wani dan takara ya janye wa wani ba, domin sai sun fara amincewa da hanyar da ta fi dacewa kafin yanke hukunci kan tsarin kawancen.

Kara karanta wannan
Shugaban kasa Tinubu ya amince a dauki sababbin sojoji 28000 da ‘yan sanda 50000 aiki
Makinde ya ce ba za su yanke shawara bisa son rai ko sha’awar wani mutum ba, domin za su yi la’akari da manufofin ’yan takara, irin ayyukan da suka yi a baya da kuma ra’ayin al’ummar Najeriya.
Wasu ’yan takara za su janye
Tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, ya bayyana cewa a shirye yake ya janye wa duk dan takarar da kawancen ya amince shi ne ya fi dacewa da shugabancin kasar.
Duke ya ce idan aka cimma matsaya kan wani mutum, zai mutunta tsarin dimokuradiyya kuma ya goyi bayan shawarar da aka yanke.
Wannan matsaya na daga cikin abubuwan da suka kara karfafa fatan cewa jam’iyyun adawa za su iya cimma yarjejeniya kan dan takara guda daya.
Sakataren yada labarai na ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya tabbatar da cewa jam’iyyarsa na cikin tattaunawar, amma ya ce ba ta yanke matsaya ba tukuna.
NDC ba za ta janye ba
Sai dai jam’iyyar NDC ta nuna rashin amincewa da yiwuwar janye wa Peter Obi, dan takararta na shugaban kasa, idan aka zabi wani dan takara daga wata jam’iyya.
Mai magana da yawun jam’iyyar, Ossai Director, ya shaida cewa muddin sauran ’yan takara, musamman Atiku, ba su janye ba, to Obi ma ba zai janye ba.
Ya ce duk da cewa jam’iyyar na jiran sanarwar wadanda suka shirya tattaunawar, ba za ta amince da wani dan takara ba in ba Obi ba.

Source: Facebook
A daya bangaren kuma, jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki ta bayyana goyon bayanta ga yunkurin samar da dan takara guda daya da zai kalubalanci APC.
Za a yi taro a Nuwamba 23
Masu shirya kawancen sun bayyana cewa taron na ranar 23 ga Nuwamba ba zai tsaya kan batun zaben dan takara guda daya kawai ba.
Ana sa ran jam’iyyun za su amince da wasu takardu guda uku da kungiyoyin aiki suka tsara bayan taron farko da suka gudanar a Abuja ranar 31 ga Agusta, 2026.
Takardun sun hada da yarjejeniyar kasa kan farfado da dimokuradiyya, tsarin hadin kan jam’iyyun adawa da kuma shirin sauye-sauyen kasa.
Hadakar ta kuma ce za a bukaci shugabannin jam’iyyun, sakatarorinsu, mambobin kwamitocin gudanarwa, kwamitocin yakin neman zabe, ’yan takarar shugaban kasa da mataimakansu su halarci taron.
A cewar mai shirya kawancen, Salihu Mohammed Lukman, halartar ’yan takara da mataimakansu da kansu zai nuna irin kudurin da suke da shi na hada kai domin amfanin kasa.
Ana hasashen Atiku zai yi nasara
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na kara kokarin neman goyon bayan al’ummar Arewa gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya yi ikirarin cewa wasu magoya bayan marigayi Shugaba Muhammadu Buhari na karkata zuwa Atiku.
Sai dai matsalolin da suka hada da tsadar rayuwa, rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki na daga cikin abubuwan da ake ganin za su iya yin tasiri kan yadda ’yan Najeriya za su zabi Atiku.
Asali: Legit.ng

