Biki Bidiri: Matashi Zai Angwance Da Kyawawan Yan Mata 2 a Rana Daya

Biki Bidiri: Matashi Zai Angwance Da Kyawawan Yan Mata 2 a Rana Daya

  • Wani matashi mai suna Prince Okebulu Ndukwo Nkobi, zai angwance da wasu kyawawan mata biyu a rana daya
  • Kamar yadda katin gayyatar bikin ya nuna, za a yi auren ne a Abiriba da ke karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia
  • Za a daura aure tare da shagalin bikin a ranar 19 ga watan Nuwamban 2023

Wani matashi dan Najeriya mai suna Prince Okebulu Ndukwo Nkobi, daga Abiriba a karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia, ya shirya tsaf domin auren wasu kyawawan yan mata biyu a rana daya.

Za a daura auren ne a ranar 19 ga watan Nuwamban 2023, a harabar gidan iyalin Nkobi da ke garin Abariba.

Matashi zai yi wuff da yan mata biyu a rana daya
Biki Bidiri: Matashi Zai Angwance Da Kyawawan Yan Mata 2 a Rana Daya Hoto: MC Clockwise
Asali: Facebook

Wani matashi mai suna MC Clockwise daga Abariba ne ya wallafa katin gayyatar auren a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani na Facebook, inda ya taya angon farin ciki.

Kara karanta wannan

Man Fetur Zai Kara Tsada a Gidajen Mai Tun da Farashin Tashoshi Ya Zarce N720

Amaren masu suna Nnenna Okeke da Aluba Itum Kalu duk sun fito ne daga yankin na Abariba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama'a sun yi martani kan matashin da zai auri mata biyu a rana daya

Amb Flownation ya ce:

"Komai zai iya faruwa a abariba."

Excellential Chukwuebuka Orji ya yi martani:

"Na taya su murna."

Daniel Wise Ndukwo ya ce:

"Zan iya rantse maku cewa duk wadannan matan ya shafe tsawon shekaru tare da su kuma yanzu ne yake son yin aure a hukumance.
"Babu wata mace sabuwar jini da ke cikin hayyacinta da za ta yarda da irin wannan auren na mutum biyu."

Ndi Mmadu Beatrice ta yi martani:

"Akwai matsala faaaa."

Princess Mercy Oteh ta ce:

"Kalli fuskokinsu ma."

Josey Andy ya ce:

"Mutum na uku da nake ganin ya yi haka a Abariba."

Chi Chi Ogisi Igara ta ce:

Kara karanta wannan

Za a Tsare Mawaka, Naira Marley da Sam Larry na Kwana 21 a Kan Mutuwar Mohbad

"Akalla dai ya fito fili ya yi abunsa ba kamar wasu da ke yin shi a boye ba."

Saurayi ya fusata yayin da budurwa ta ki ziyartarsa bayan ya tura mata kudin mota

A wani labari na daban, wata yar TikTok mai suna @_halfgirlfriend ta saki hoton hirarsu da wani mutumi wanda ya aika mata da kudin mota.

Sai dai kuma, da gangan ta ki zuwa kuma hakan ya fusata matashin wanda ya yi martani nan take.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel