Wani Mutum Ya Fasa Ihu Bayan Ya Kama Mai Aikinsa Tana Wanke Masa Laftof Da Kayan Wuta Da Sabulu

Wani Mutum Ya Fasa Ihu Bayan Ya Kama Mai Aikinsa Tana Wanke Masa Laftof Da Kayan Wuta Da Sabulu

  • Wani dan Najeriya ya shiga gida ya ga mai aikinsa tana wanke masa kayan wuta da sabulu da ruwa kuma hakan ya firgita shi
  • Mutumin ya caccaki matar yayin da ta kai kan laftof dinsa, cewa duk sun yi kura kuma suna bukatar wanki
  • Bidiyon da ke nuna lokacin da ya kama mai aikin ya yadu a soshiyal midiya kuma ya bai wa mutane dariya sosai

Wani dan Najeriya ya cika da mamaki bayan ya kama mai aikin gidansa tana yin ayyuka ba yadda ya kamata ba.

A cikin bidiyon da ya yadu a TikTok, mutumin ya shigo sai ya tarar da matar tana amfani da ruwa da sabulu wajen wanke kayan wutan gidan.

Mai aiki ta wanke kayan wuta da sabulu
Wani Mutum Ya Fasa Ihu Bayan Ya Kama Mai Aikinsa Tana Wanke Masa Laftof Da Kayan Wuta Da Sabulu Hoto: @kelvinthehustler12
Asali: TikTok

"Hajiya, me kike yi?" mai gidan da ya kadu ya tambayi mai aikin, inda ta amsa da cewar kayan wutan sun yi kura.

Kara karanta wannan

Wani Mutum Ya Baje Kolin Gidan Da Yake Haya, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Nan take mutumin ya hau ta da fada cikin fushi amma sai matar ta tsaya kan bakarta kuma har ta fara wanke laftof dinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya daka mata tsawa yayin da bidiyon ya kai karshe. Bidiyon wanda @kelvinthehustler ya yada ya samu mutum fiye da 580k da suka kalla kuma abun ya ba su mamaki.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

AUTHORITY ONE ya ce:

"Waoooo. Ta burge ni don Allah ka taimaka mun da daya domin gidana cike yake da kura."

ENOCH WHITE ya ce:

"Na ga cewa laftof din ya fi sauran muhimmanci kalli irin gudun da ya yi don dauke laftof din."

fidel_eto ta ce:

"Gwanda ka ajiye wannan wayar sannan ka fara busar da su ka san nawa ka kashe kan wadannan kayan wutan."

Hayatu ya ce:

"Tana da niya mai kyau. Don Allah ka yi mata karin albashi."

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kwararawa Malalacin Mijinta Ruwa Yana Cikin Bacci, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

Maurine Thumi:

"Ta cancanci kari....tana da kwazon aiki."

Ann ta ce:

"Da ace ka yi amfani da lokacin da ka kashe wajen saita kamararka don dakatar da ita...,da gidanka bai cike ba."

Bidiyon yan mata a kan babura ya dauka hankali

A wani labari na daban, mun ji cewa jama'a sun yi cece-kuce yayin da wani bidiyo da ke nuna wasu yan mata suna tuka babura cike da farin ciki ya yadu a soshiyal midiya.

Daya daga cikin yan matan, @user1868198263041, ta yada hadadden bidiyon a dandalin sada zumunta na TikTok.

Asali: Legit.ng

Online view pixel