Tinubu Kadu, Ya Bada Umarnin a Ceto Daliban Jami’ar Gusau Tsageru Suka Sace a Zamfara

Tinubu Kadu, Ya Bada Umarnin a Ceto Daliban Jami’ar Gusau Tsageru Suka Sace a Zamfara

  • Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, zai tabbatar da an dawo da daliban da aka sace a jami’ar Gusau
  • An ruwaito yadda tsageru suka kutsa dakin kwanan dalibai tare da yin awon gaba da wasu dalibai da basu ji ba basu gani ba
  • Ba wannan ne karon farko da ake sace dalibai a makarantun jihar Zamfara ba, an sha yin hakan a lokuta da dama

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su kubutar da sauran daliban jami’ar tarayya ta Gusau da ‘yan ta’adda suka sace a ranar Alhamis din da ta gabata.

Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja cewa, Tinubu ya yi Allah-wadai da abin da ya faru na sace daliban.

Kara karanta wannan

Ahaf: Tinubu ya dawo da 'yan Najeriya baya cikin bakin talauci sadda ya cire tallafin mai, malamin jami'a

Ya kara da cewa shugaban kasar ya ce babu wata hujja ta da’a ga irin wannan danyen aikin da aka yi wa wadanda ba su ji ba ba su gani ba, rahoton Vanguard.

Tinubu ya ba da umarnin a ceto daliban Zamfara
An sace dalibai a Zamfara, Tinubu ya dauki mataki | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Zan tabbatar da an ceto dalibai, Tinubu

Shugaban ya tabbatar wa iyalan daliban da aka sace cewa ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an dawo musu da yaransu da aka sace.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu ya yi alkawarin cewa, Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da cewa cibiyoyin ilimi sun kasance wuraren ba da ilimi, ci gaba, da ba da dama, kuma ta tabbatar da ayyukan ta’addanci basu kai ga lalata manufar ilimi ba.

Yadda aka sace daliban a jami’a

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki dakunan kwanan dalibai mata uku a Sabon Gida, inda daliban ke zama a wajen babban harabar jami’ar da tsakar daren ranar Alhamis, inda suka yi awon gaba da daliban da ba a san adadinsu ba.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Malaman jami'a sun ci taliyar karshe saboda aikata badala da rashawa

An yi garkuwa da dalibai mata da yawa, amma wasu sun tsere, kamar yadda rahotanni suka bayyana a kwanan nan, Daily Nigerian ta tattaro.

Jihar Zamfara na daga jihohin da ake yawan samun barnar ‘yan ta’adda masu rike da makamai a Arewa masu Yammacin Najeriya.

An sace dalibai a Zamfara

A wani labarin, an rahoto cewa yan bindiga sun sace wasu dalibai hudu yayin da suke dawowa daga daurin wani abokinsu a kan hanyar Kaura Namoda da Birnin Magaji a Zamfara, rahoton Premium Times.

Wadanda abin ya faru da su da aka ce daliban Kwalejin Fasahar Lafiya ne ta Tsafe, sun halarci daurin auren ne tare da wasu yan uwansu uku da aka sace su.

Mohammed Shehu, kakakin yan sandan jihar Zamfara ya tabbatar cewa an sace wasu mutane a kan hanyar Kaura Namoda da Birnin Magaji a ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel