Gwamnatin Tinubu Ta Makaryata Ne da Mayaudara, Na Hannun Daman Atiku Ya Kunto Kura

Gwamnatin Tinubu Ta Makaryata Ne da Mayaudara, Na Hannun Daman Atiku Ya Kunto Kura

  • Ana zargin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da tafka karya da yada farfagandar da bata dace ba ko kadan
  • Phrank Shaibu, mai magana da yawun Atiku Abubakar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 24 ga watan Satumba.
  • Shaibu ya yi kira ga kafafen yada labarai a Najeriya da su rika tantance gaskiyar ikirarin da gwamnatin Tinubu ke yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Phrank Shaibu, mataimaki na musamman kan hulda da jama’a ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya lissafo karairayi goma da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta yi.

Shaibu ya bukaci kafafen yada labaran Najeriya da su rika bin diddigin duk wani ikirarin da gwamnatin Tinubu ta yi don taimakawa wajen tabbatar da amincin ‘yan kasa, in ji rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

An tafka asara yayin da gobara ta lamushe fitaccen kamfanin robobi a jihar kasuwanci

Gwamnatin Tinubu ta mayaudara ce
Gwamnatin yaudara ce gwamnatin Tinubu, inji PDP | Hoto: | Hoto: Atiku Abubakar/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cewar hadimin na Atiku:

“Shawarata ga kafafen yada labarai na Najeriya ita ce su rika bin diddigin duk wani ikirarin da wannan gwamnati za ta yi domin hakan ne zai taimaka wajen tabbatar da nagartarsu. Idan gwamnatin Tinubu ta ce gari ya waye, ku fita waje don tantance ko rana ta fito.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 24 ga watan Satumba.

Karyar da ake zargin gwamnatin Tinubu ta yi

A cewar mai magana da yawun Atiku, wadannan su ne da yawan karairayin da gwamnatin shugaba Tinubu ta yi ya zuwa yanzu tun bayan hawa mulki:

“Karya ta farko da Bola Tinubu ya yi ita ce a jawabinsa na farko, inda ya bayyana cewa tallafin man fetur ya kau.
“Karya ta biyu da wadannan ’yan baranda suka yi ita ce, Hadaddiyar Daular Larabawa ta dage takunkumin hana ‘yan Najeriya shiga kasar nan take kuma wai duk ‘yan Najeriya suna da ‘yancin zuwa Dubai.

Kara karanta wannan

Rikici: Magana Ta Ƙare, Gwamnan PDP Ya Ƙori Mataimakin Gwamna Daga Gidan Gwamnati, Sanarwa Ta Fito

“Karya ta uku da wannan gwamnatin yaudara ta yi ita ce, Tinubu ne shugaban Afrika na farko da ya buga kararrawa NASDAQ. Alhali shugaban kasar Malawi, Jakaya Kikwete, ya taba buga kararrawar a ranar 21 ga Satumba, 2011.
“Wata karyar kuma ita ce sanarwar da Ajuri Ngelale ya fitar a ranar 27 ga Agusta, 2023, inda aka ruwaito jakadan shugaban Amurka kuma mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Ambasada Molly Phee yana cewa, ‘Shugaba Joe Biden na neman ganawa da kai kan batun UNGA kuma kai kadai ne shugaban Afirka da ya bukaci ganawa da shi. Wannan alama ce ta babban darajarsa da tsarin shugabancin ka.’ To, wannan dai karyace kuma abin kunya, kasancewar Tinubu ya bar UNGA bai gana da Shugaba Biden ba.
"Karya ta biyar ita ce ikirarin da Tinubu ya yi a NASDAQ inda ya bayyana cewa 'Mun canza farashin musayar kudi zuwa wani adadi mai kyau, abin dogaro da ke gogayya da Naira."

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi Da Musulmi: “Kana Fifita Yarbawa Da Kiristoci”, MURIC Ta Caccaki Tinubu Kan Nadin Mukamai

Zuwan Tinubu Dubai

Shugaban kasa Bola Tinubu zai gana da shugabannin hadaddiyar daular Larabawa (UAE) a yayin wani yada zangon da zai yi a birnin Abu Dhabi na na kasar ta UAE.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa za a gudanar da ganawar ne domin warware matsalolin diflomasiyya da ke tsakanin kasashen biyu.

Matsalolin sun hada da hana biza da kasar ta sanya akan 'yan Najeriya tun watan Oktoban 2022 da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na Emirates zuwa Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel