Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Yi Kaca-Kaca da Fitaccen Kamfanin Robobi a Jihar Legas

Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Yi Kaca-Kaca da Fitaccen Kamfanin Robobi a Jihar Legas

  • An bayyana yadda gobara ta yi kaca-kaca da wani sashe na kamfanin robobin Mega Plastics a jihar Legas da ke Kudancin Najeriya
  • Ana fargabar gobarar ta jawo asarar dukiya mai yawa yayin da aka yi sa’a ba a samu asarar rai ko jikkata ba
  • An yawan samun matsalolin tashin gobara a yankuna daban-daban na Najeriya, akan tafka asarar dukiya da rayuka

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Legas - Wani sashe na wani kamfanin robobin Mega Plastics dake unguwar Ilupeju a Legas, ya kone kurmus da sanyin safiyar yau Asabar, 23 ga Satumba 2023.

Labarin na zuwa ne a cikin wata sanarwar da ta fito ta hannun Daraktan Hulda da Jama’a da Wayar da Kan Jama’a na Hukumar LASTMA, Adebayo Taofiq, rahoton Punch.

A cewar sanarwar, jami’an LASTMA sun isa wurin da gobarar ta tashi da misalin karfe 6:30 na safe, inda suka tuntubi sauran jami’an bayar da agajin gaggawa don taimakawa wajen kashe gobarar.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Yaron Da Hanjinsa Suka Bace Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Gobara ta kone kamfanin roba
Kamfanin robobi ya kone a Legas | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ta yaya gobarar ta tashi?

Yayin da ba a iya gano musabbabin tashin gobara a masana’antar ba, hukumar ta bayyana cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa gobarar ta shafi ma’ajiyar kamfanin ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran kungiyoyin masu ba da agajin gaggawa da suka ba da agaji a wurin sun hada da hukumar kashe gobara ta tarayya da jihar, ‘yan sanda da kuma sashin ba da agajin gaggawa na Lasema.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, ba a samu labarin wani ya jikkata ko yam utu ba har zuwa lokacin da hada wannan rahoton, The Guardian ta naqalto.

Ana yawan samun tashin gobara a kamfanoni da kuma wuraren sana’o’I daban-daban a Najeriya, lamarin da ke jawo asarar dukiya mai tarin yawa ga ‘yan kasuwa ga gwamnatoci.

Shaguna sun kone a Legas

A wani labari na daban, an samu mummunar asara yayin da wasu shaguna sama da 10 suka kone kurmus a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: An Kama a Wani Mutumi da Ake Zargi da Lalata da Ɗiyarsa, Ta Mutu a Yanayi Mai Mamaki

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar kashe gobara ta ba da labarin gaskiyar abin da ya faru da kuma mafitar da suka samo a kai.

Jihar Kano na daga jihohin da ake yawan samun tashin gobara a lokuta daban-daban saboda cunkoso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel