Ban mutu ba, Tinubu ya bayyana yayin da ya isa Najeriya daga Dubai

Ban mutu ba, Tinubu ya bayyana yayin da ya isa Najeriya daga Dubai

  • Asiwaju Bola Tinubu a ranar Talata, 15 ga watan Yuni, ya iso kasar daga Dubai bayan ya kwashe kwanaki a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE)
  • Rahotanni sun bayyana cewa shugaban na APC ya tafi Dubai ne sakamakon wani hatsarin gida da ya samu a bandakinsa makonnin da suka gabata
  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni, ya ziyarci jihar Legas don kaddamar da wani aikin jirgin kasa amma Tinubu bai kasance a taron ba

Bayan jita-jita game da mutuwarsa, shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya isa Legas daga Dubai a daren ranar Talata 15, ga watan Yuni.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa kafafen sada zumunta sun cika da jita-jitar cewa Tinubu ya mutu, amma ofishin sa na yada labarai ya karyata rahotannin, yana mai cewa tsohon gwamnan zai iso kasar nan bada dadewa ba.

KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Ba zai yiwu ka mayar da aikinka wuyan jihohi ba, Gwamna Wike ga Buhari

Ban mutu ba, Tinubu ya bayyana yayin da ya isa Najeriya daga Dubai
Babban jigon APC, Asiwaje Bola Tinubu yayin da yadawo daga tafiya Hoto: PM News.
Asali: UGC

Legit.ng ta tattaro cewa Tinubu ya isa Legas cikin koshin lafiya, ya kunyata wadanda ke masa fatan mutuwa.

A cewar rahoton, watakila jita-jitar mutuwar Tinubu ya kara ruruwa ne sakamakon hatsarin cikin gida wanda rahotanni suka ce ya yi a bandakinsa makonni biyu da suka gabata.

An ce Tinubu ya fadi a kan gwiwoyinsa biyu kuma ya samu rauni, wanda hakan ya sanya tafiyarsa zuwa Dubai don neman lafiya.

KU KARANTA KUMA: Buhari zai ziyarci Borno, zai kaddamar da gidaje 4,000 na 'yan gudun hijira, Zulum

Asiwaju Tinubu baya nan yayin da Shugaba Buhari ya kai ziyara Legas

Jaridar The Punch ta kuma ruwaito cewa Tinubu bai halarci taron ranar Alhamis, 10 ga watan Yuni ba, lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci Legas kuma ya kaddamar da wasu ayyuka.

A gefe guda, mun ji cewa wasu masoyan jagoran jam’iyyar APC a kudancin Najeriya, Asiwaju Ahmed Tinubu, sun shigo birnin Abuja dauke da hotunan neman takararsa a 2023.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto a ranar Litinin 14 ga watan Yuni, 2021, cewa magoya-bayan tsohon gwamnan na jihar Legas sun cika gari da hotunansa.

A ranar Lahadi wadannan mutane su ka shiga lika hotunan neman takarar shugaban kasar Bola Tinubu a wuraren da aka san zai dauki hankalin jama’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel