Edo: Magana Ta Kare, Gwamna Obaseki Ya Aike da Wasika Ga Mataimakinsa

Edo: Magana Ta Kare, Gwamna Obaseki Ya Aike da Wasika Ga Mataimakinsa

  • Taƙaddama kan canja wa mataimakin gwamnan jihar Edo ofis daga gidan gwamnati zuwa wani wuri ta zo ƙarshe
  • Da safiyar ranar Talata, wasiƙar sanar da mataimakin gwamna canjin da aka samu ta bayyana
  • An jima ba a ga maciji tsakanin Philip Shaibu da maigidansa gwamna Godwin Obaseki na PDP

Jihar Edo - Ga dukkan alamu dirama da kace-nace kan sauya wa mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ofis ta zo ƙarshe bayan sanarwa a hukumance ta bayyana.

Takardar sanarwan mai ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Edo, Osarodion Ogie, ta fito ne ranar Talata da safe, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Gwamna Obaseki tare da mataimakinsa, Shaibu.
Edo: Magana Ta Kare, Gwamna Obaseki Ya Aike da Wasika Ga Mataimakinsa Hoto: Godwin Obaseki
Asali: Twitter

Idan baku manta ba mataimakin gwamna, Shaibu ya musanta labarin sauya masa Ofis a ranar Litinin da ta gabata, a lokacin da ya taras an kulle ofishinsa na cikin gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Majalisa Ta Fara Shirin Tsige Mataimakin Gwamnan APC Daga Kujerarsa? Gaskiya Ta Fasu

Ya kuma bayyana cewa ba a kai masa wasikar barin harabar gidan gwamnati zuwa wani waje daban ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mataimakin gwamnan ya kuma ce ma’aikatan ofishinsa ne kawai aka ba su umarni ta hanyar wasika cewa su koma sabon ofishin, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Takardar canja ofishin Shaibu ta bayyana

Wasiƙar Sakataren gwamnati, mai ɗauke da adireshin mataimakin gwamnan, ta ce Gwamna Godwin Obaseki, ya umarci Shaibu ya tattara ya bar gidan gwamnati ya koma sabon ofishinsa.

Wasiƙar mai ɗauke da kwanan watan 15 ga watan Satumba, 2023, ta isa wurin babban Sakataren Ofishin mataimakin gwamna ranar Litinin, 18 ga watan Satumba.

Ɗauke da taken, "Sanarwan sauya wurin zaman Ofis," Wasiƙar ta ce:

"Na rubuta wannan takarda ne domin sanar da kai cewa mai girma Gwamna ya amince da mayar da ofis dinka zuwa No 7, Dennis Osadebey Avenue, G.R.A., cikin birnin Benin."

Kara karanta wannan

Manyan Hadiman Gwamna da Wasu Jiga-Jigai Sun Ƙara Yi Wa PDP Babban Lahani, Sun Koma APC

"Saboda haka ana buƙatar ka tabbatar da bin wannan umarni bisa amincewar Gwamna, don Allah."

Yadda rikici ya shiga tsakanin gwamna da mataimakinsa

Shaibu ya fara takun saƙa da gwamna Obaseki ne lokacin da ya shigar da ƙara a gaban babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja a farkon watan Agusta.

Mataimakin gwamnan ya shigar da ƙarar Ubangidansa ne yana roƙon Kotu ta ba shi ƙariya daga shirin gwamna na amfani da majalisar dokoki wajen tsige shi.

Nan take gwamna Obaseki ya maida martani, inda ya kori baki ɗaya masu taimaka wa Shaibu na ɓangaren midiya kana ya canza masa ofis zuwa wani wuri daban.

Wasu fitattun ‘yan jihar daga bangaren siyasa da na addini, sun shiga tsakani makonni uku da suka gabata, wanda ya sanya Shaibu janye karar daga kotu.

Malamin Addini Ya Gargadi Atiku da Obi, Ya Ce Guguwar Sauya Sheka Na Nan Tafe Ga LP da PDP

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tashin Hankali Bayan Gwamnan PDP Ya Hana Mataimakinsa Shiga Ofis

Kuna da labarin Shugaban Cocin INRI, Primate Elijah Ayodele, ya ce ya hango gagarumar guguwar sauya sheƙa da ke shirin turnuƙe Labour Party.

Malamin cocin ya ƙara da bayanin cewa idan guguwar ta zo zata haɗa da babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa watau PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel