Ragon layya N300K: Dillalai sun yi tagumi, jama'a ba sa zuwa sayen raguna

Ragon layya N300K: Dillalai sun yi tagumi, jama'a ba sa zuwa sayen raguna

  • Farashin dabbobi a Najeriya ya yi matukar tashi idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata ta babbar sallan 2021
  • 'Yan kasuwa sun koka kan yadda jama'a ba sa yawan sayen dabbobi duk da cewa kwanaki kadan ya rage a yi bikin sallah
  • A bangare guda, mun tattaro farashin da kasuwanni ke sayar da dabbobin layya, inda aka shaida tashin kayan kai tsaye

Najeriya - Farashin raguna ya karu sosai a duk fadin kasar nan gabanin bikin Eid-el-Kabir (babbar Sallah) na wannan shekara 2023.

A kasuwar Oluwaga da ke unguwar Ipaja a jihar Legas, ana sayar da kananan raguna daga N80,000 zuwa N100,000, matsakaita kuwa tsakanin N120,000 zuwa N180,000, ana sayar da manyan raguna daga N250,000 zuwa N350,000.

Tashin farashin raguna ya sa dillalai zulumi a Najeriya
Ragon layya N300K: Dillalai sun yi tagumi, jama'a ba sa zuwa sayen raguna | Hoto: thecable.com
Asali: UGC

Wani dillalin rago a kasuwar, wanda ya bayyana sunansa da Muhammad, ya shaidawa TheCable cewa farashin raguna ya tashi matuka saboda farashin sauran kayayyakin ma ya tashi.

Ya koka da yadda kudin jigilar dabbobin daga Kano ma ya karu idan aka kwatanta da na bara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

“Na kawo su ne daga Kano. Diesel ya yi tsada. Kawo su nan yana daukar kudi da yawa. Abincinsu ma ya yi tsada.
“Wani lokaci, wadannan dabbobin suna rashin lafiya, kuma dole ne mu yi musu magani. Ina nemo likita ya zo nan ya yi musu allura.

Ya ce duk da tsadar kayayyaki, jama'a na saye, inda ya ce wasu kwastomomi sun riga sun sayi ragunansu, kawai jira suke jajiberin Sallah su dauka.

A kasuwar unguwar Abesan, farashin kananan raguna ya tashi daga N65,000 zuwa N80,000, matsakaita daga N150,000 zuwa N180,000, yayin da manyan raguna suka tashi daga N250,000 zuwa N300,000.

Haka kuma farashin shanu ya tashi daga tsakanin N450,000 zuwa N550,000 a Legas.

Faruq wani dillalin shanu a kasuwar ya ce karin farashin abincin dabbobi ne ya haifar da hauhawar farashin raguna da shanu.

A cewarsa:

"Kula da wadannan dabbobi ba abu ne mai sauki ba."

Duk da karancin saye, ya bayyana fatansa cewa zai sayar da dukkan dabbobinsa kafin karshen mako.

Jihar Benin

A cikin birnin Benin, dillalan raguna sun damu da rashin sayen kayansu yayin da kasar ke shaida tsadar kayan yanka.

A wani rahoton da NAN ta fitar, an sayar da raguna daga N80,000 zuwa sama a kasuwar Shanu ta 2+2 Cattle Market da ke Eyaen.

Shugaban kasuwar shanu Aliko Haruna ya bayyana cewa tsadar kayayyaki na alaka ta kai tsaye da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki kai tsaye.

Shugaban ya ce ba daidai ba ne a dora alhakin rashin tsaro a yankin Arewa da lamarin tsadar dabbobi.

Jihar Oyo

A ranar Laraba ne wani dillalin rago ya shaidawa jaridar TheCable cewa farashin kan kai N70,000 zuwa N300,000 ya danganta da yadda ciniki ya kaya da kuma girman dabbar.

A Ibadan, ya ce kananan raguna suna kai N70,000 yayin da matsakaita da manya ake sayar da su tsakanin N120,000 zuwa N300,000.

Jihar Neja

A jihar Neja kuwa, farashin dan karamin rago ya kan kai N50,000 zuwa N60,000.

Ana sayar da masu matsakaicin girma tsakanin N80,000 zuwa 100,000, yayin da manyan raguna kuwa ke kai N120 zuwa N150,000.

Babbar birnin tarayya, Abuja

A Abuja karamin rago kan kai N70,000 yayin da babba ke kai tsakanin N200,000 zuwa N300,000.

Jihar Kaduna

A Kaduna dai, da alama yanayin bai yi wa wasu Musulmi dadi ba. Da suka zanta da wakilin jaridar Leadership sun ce sun kadu da ganin yadda raguna suke masifar tsada.

Ziyarar da aka kai shahararriyar Kasuwar Shanu a Jihar, Kasuwar Zango, Tudun-Wada da Kaduna, matsakaicin rago wanda a bara bai wuce N70,000 zuwa N80,000 ba, yanzu ana sayar da shi tsakanin N100,000 zuwa N150,000. .

Bikin babban sallah: Gwamna Ganduje ya baiwa makarantu hutun kwanaki 10

A wani labarin, gwamnatin jihar Kano a ranar Laraba, 6 ga watan Yuli, ta baiwa daliban makarantun firamare da na sakandare hutun kwanaki 10 domin bikin babban Sallah, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar ilimi ta jihar, Aliyu Yusuf ya saki, ya ce hutun zai fara daga ranar Alhamis, 7 ga watan Yuli zuwa Lahadi, 17 ga watan Yuli.

Yusuf ya yi kira ga iyaye da masu kula da daliban makarantun da su lura da umurnin, Nigerian Tribune ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel