Bikin babban sallah: Gwamna Ganduje ya baiwa makarantu hutun kwanaki 10

Bikin babban sallah: Gwamna Ganduje ya baiwa makarantu hutun kwanaki 10

  • Dalibai a makarantun firamare da na sakandare a jihar Kano za su tafi hutun kwanaki 10 don bikin babban sallah
  • Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ce ta bayar da wannan sanarwar a cikin wani jawabi da ta saki a ranar Laraba, 6 ga watan Yuli
  • Kamar yadda kakakin ma’aikatar ilimi ta jihar, Aliyu Yusuf ya bayyana, hutun zai fara ne daga Alhamis, 7 ga watan Yuli zuwa Lahadi, 17 ga watan Yuli

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Gwamnatin jihar Kano a ranar Laraba, 6 ga watan Yuli, ta baiwa daliban makarantun firamare da na sakandare hutun kwanaki 10 domin bikin babban Sallah, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar ilimi ta jihar, Aliyu Yusuf ya saki, ya ce hutun zai fara daga ranar Alhamis, 7 ga watan Yuli zuwa Lahadi, 17 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan ISWAP sun fitar da bidiyo, sun ce su suka kai farmaki magarkamar Kuje

Abdullahi Ganduje
Bikin babban sallah: Gwamna Ganduje ya baiwa makarantu hutun kwanaki 10 Hoto: Thisday
Asali: UGC

Yusuf ya yi kira ga iyaye da masu kula da daliban makarantun da su lura da umurnin, Nigerian Tribune ta rahoto.

A cewarsa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Don haka, ma’aikatar ta yi umurnin cewa dukkanin daliban SS3 da ke zana jarrabawar NECO, NABTEB da NBAID da kuma daliban da suke shirin musanya daga wasu jihohi a GSS Gwarzo da GGSS Shekara su ci gaba da kasancewa a makarantunsu.
“Hakazalika ma’aikatar ta umurci dukkanin shugabannin makarantun firamare da sakandare da su tabbatar da cewa daliban makarantun kwana sun dawo a ranar Lahadi, 17 ga watan Yuli yayinda yan makarantun jeka ka dawo za su koma ajujuwa a ranar Litinin, 18 ga watan Yuli, domin za a fara harkokin karatu a ranar da aka dawo.
“Sai dai kuma, ma’aikatar na gargadin cewa za a dauki matakin da suka dace kan daliban da suka saba.”

Kara karanta wannan

Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

Eid-el-Kabir: Yan Sanda Sun Kama Wasu Mutane 2 Saboda Satar Ragon Sallah

A wani labarin, mun ji cewa yan sanda a jihar Ogun sun tsare wasu mutane biyu kan zarginsu da satar ragon babban sallah, Leadership ta rahoto.

Eid el Kabir, da aka fi kira da babban sallah a Najeriya zai fado ne a ranar Asabar 9 ga watan Yulin 2022.

A cikin sanarwar da ya fitar, kakakin yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi, ya ce an kama wadanda ake zargin na Adetunji Alagbe da Opeyemi Ogunlokun, kan satar ragon wani Sodiq Abolere a Ogijo a Ikorodu Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel