Harin Kuje: Kun Bani Kunya, Buhari Ya Fada Wa Hukumomin Tattara Bayanan Sirri

Harin Kuje: Kun Bani Kunya, Buhari Ya Fada Wa Hukumomin Tattara Bayanan Sirri

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya ce hukumomin tattara bayanan sirri na Najeriya sun bashi kunya saboda yadda yan ta'adda suka shirya suka kai hari
  • Shugaban kasar ya bayyanan hakan ne yayin da ya kai ziyara gidan yarin Kuje da ke Abuja inda yan ta'addan suka kai hari
  • Buhari ya yi wasu muhimman tambayoyi game da afkuwar harin ya kuma bukaci a tattara masa cikakken bayani a tura masa

FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna rashin jin dadinsa da hukumomin tattara bayanan sirri, bayan harin da yan ta'adda suka kai gidan yarin Kuje, Daily Trust ta rahoto.

Bayan zagawa ya duba wurin da aka kai harin a ranar Laraba, "hukumomin tattara bayanan sirri sun bani kunya. Ta yaya yan ta'adda za su shirya, su taho da makamai, su kai hari wurin da jami'an tsaro suke kuma su tsere?

Kara karanta wannan

Femi Falana ya Bukaci gwamnati tarayya da ta sauya fasalin tsaro a kasar

Buhari a Kuje
Harin Kuje: Kun Bani Kunya, Buhari Ya Fada Wa Hukumomin Tattara Bayanan Sirri. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Garba Shehu, kakakin Buhari, "jim kadan bayan shi (Buharin) ya isa, sakataren dindindin na ma'aikatar harkokin cikin gida, Dr Shuaib Mohammed Lamido kuma Kwantrola Janar na NCoS, Haliru Nababa, sun nuna masa wurin da aka saka bam, da ofisoshi da aka kona, ya kara da cewa daga bisani maharan sun kai hari inda aka ajiye yan ta'addan na Boko Haram.
"An fada wa shugaban kasar cewa daga karshe, ba a gano kowa cikin yan ta'addan 63, amma an jadada cewa akwai bayanansu saboda an ajiye kwafi a intanet."
Shehu cikin sanarwar ya ce Buhari ya yi mamakin harin inda ya yi wasu tambayoyi: "Ta yaya masu tsaron gidan yarin suka gaza dakile harin? Fursunoni nawa ke gidan yarin?
"Guda nawa suka rage a yanzu? Jami'ai nawa ke aiki a ranar? Nawa cikinsu ke da makamai? Masu gadin gidan yarin sun hau kan husumiya? Kyamarar tsaro tana aiki?."

Kara karanta wannan

Da dumidumi: Kimanin fursunoni 600 sun tsere bayan yan Boko Haram sun farmakin gidan yarin Kuje – FG

Ya ce an kuma sanar da shugaban kasar cewa an kamo fursunoni 350 cikin wadanda suka tsere yayin da 450 har yanzu ana nemansu.

Daga bisani Shugaba Buhari ya bukaci a tattara cikkaken abin da ya faru a tura masa.

Buhari ya yi martani kan masu sukar ziyarar da zai tafi Senagel duk da harin Kuje

Yayin martani kan sukar da ake yi ga tafiyarsa zuwa Dakar, Senegal, Shugaban kasar ya ce:

"Gwamnatoci ba su dena aiki saboda suna fama da barazanar yan ta'adda.
"Idan aka soke ziyarar ta Senegal na nufin yan ta'addan sunyi nasara wurin kwace kasar, hakan kuma abu ne da babu gwamnati mai tsaye da kanta da za ta bari ya faru."

Asali: Legit.ng

Online view pixel