Zargin almundahana: Kotu ta ba Sanata Okorocha izinin tafiya jinya kasar waje

Zargin almundahana: Kotu ta ba Sanata Okorocha izinin tafiya jinya kasar waje

  • Babbar kotun Abuja ta ba da dama ga sanata Rochas Okorocha ya tafi kasar waje neman lafiya kamar yadda ya nema
  • Kotun ta kuma gindaya sharadi, ta ce idan ya yi amfani da hakan ya tsere za ta dauki mataki mai tsauri a kansa
  • Ana zargin Okorocha ne da yin kwana da wasu kudade mallakin kasa, kamar yadda EFCC ta gabatar a kotu

Abuja - A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha izinin tafiya kasar Burtaniya domin neman lafiyarsa.

Mai shari’a Inyang Ekwo, wanda ya ba da izinin, ya umarci magatakardar kotun da ya ba shi fasfo dinsa domin fara shirin ziyarar ta jinya, Punch ta ruwaito.

Kotu ta ba da belin Rochas Okorocha
Almundahana da kudin kasa: Kotu ta ba Sanata Okorocha izinin tafiya jinya kasar waje | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Umurnin Alkalin ya biyo bayan bukatar da wani babban lauya, Mista Ola Olanipekun ya yi, wanda ya shaida wa kotun cewa wanda yake karewa na fama da matsalolin lafiya a yanzu.

Kara karanta wannan

Ya kamata ka girmi siyasar kabilanci: Peter Obi ya caccaki Kwankwaso

Ya kara da cewa Okorocha, wanda yanzu Sanata ne mai wakiltar Imo ta Arewa a majalisar dattawa, ba zai lalata wannan dama da ya samu ba, kuma zai dawo kasar domin ci gaba da shari’arsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ko da yake, hukumar EFCC da Chile Okoroma ta wakilta, ta nemi yin adawa da wannan batu, lokacin da alkali ya bayyana yiwuwar ba da belin.

Yayin da yake amsa bukatar, mai shari’a Ekwo ya umarci Okorocha da ya mayarwa magatakardar kotun fasfo din nasa kasa da kwanaki uku da dawowarsa Najeriya.

Alkalin ya ce zai ayyana neman Okorocha ruwa a jallo idan ya yi yunkurin bata damar da aka ba shi, rahoton Daily Sun.

Daga nan ne mai shari’a Ekwo ya sanya ranar 7 ga watan Nuwamba domin ci gaba da shari’arsa kan tuhume-tuhumen da gwamnatin tarayya ta gabatar.

Kara karanta wannan

Okupe: Abin da ya sa tun tuni Peter Obi ya yi watsi da maganar dunkulewa da Kwankwaso

Jami'an EFCC sun tasa keyar sanata Okorocha daga gidansa

A wani labarin, hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama Sanata Rochas Okorocha a gidansa ta tafi dashi.

Hukumar ta kutsa kai cikin gidan nasa ne bayan da aka ji karar harbe-harbe a wajen, kamar yadda rahotanni suka bayyana a baya.

EFCC ta kuma dage cewa dole ne ‘yan jarida su fice daga harabar gidan, tare da korar duk wanda ke gidan da karfi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel