Ya kamata ka girmi siyasar kabilanci: Peter Obi ya caccaki Kwankwaso

Ya kamata ka girmi siyasar kabilanci: Peter Obi ya caccaki Kwankwaso

  • Peter Obi ya fadi maganganu masu dumi kan bayanan Kwankwaso game da zaben mutumin Kudu maso Gabas
  • Peter Obi ya kuma bayyana cewa, shi ne masanin matsalolin Najeriya, kuma ya kamata a ba shi damar mulkar Najeriya
  • A bangare guda, ya ce, Najeriya na halin da take a yanzu ne saboda tsauraran akidun jama'a na kabilanci

Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, ya yi kira ga takwaransa na jam'iyyar NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso, da ya girmi batun kabilanci.

Obi ya bayyana haka ne a martanin da Kwankwaso ya yi a baya na cewa Arewa ba za ta goyi bayan duk wani dan takara daga Kudu maso Gabas a 2023 ba.

A wata hira da yayi da Arise TV a ranar Laraba, 6 ga watan Yuli, tsohon gwamnan na Anambra ya bayyana cewa saboda kalamai irin wannan ne Najeriya ta kasance inda take ta fuskar tsaro, ilimi, da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Peter Obi: A madadin kwararru, 'yan tasha ne ke tafiyar da lamurran kasar nan

Peter Obi ya caccaki Kwankwaso
Ya kamata ka girma: Peter Obi ya caccaki Kwankwaso kan siyasar kabilanci | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Dan siyasar na yankin Kudu maso Gabas ya ce yana son ‘yan Najeriya su zabe shi ba tare da la’akari da kabilarsa ba saboda ya san mafita ga halin da al’ummar kasar ke ciki kuma a shirye yake ya magance SU.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cikin hirar da New Telegraph ta samo, ya ce:

"Maganganun da Kwankwaso ya yi su ne dalilan da suka sa muke da 'yan Najeriya miliyan 100 cikin talauci, da duk kalubalen da muke ciki a matsayinmu na kasa, da kuma dalilin rashin tsaro a Najeriya saboda maimakon zabar cancanta, muna zabe ne bisa tushen kabilanci.
“Ku nuna min inda za ku sayi abinci mai rahusa saboda ku daga kudu maso gabas, kudu maso yamma, da arewacin Najeriya kuke.
“Jami’o’inmu a rufe suke amma muna maganar kabilanci.
“Ba na son mutane su zabe ni saboda ni Igbo ne, daga Kudu maso Gabas; kawai ku zabe ni domin ni dan Najeriya ne mai son ceto kasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Bana son tsohon hannu ya zama mataimakina, na fi son matashi mai jini a jika, Peter Obi

“Kwankwaso ya ce ina da masaniyar matsalar kasar nan wato tattalin arziki amma duk da haka yake so in zama mataimakin shugaban kasa: to me ya sa ba zan iya zama dan takarar shugaban kasa ba don aiwatar da mafitar? Bari in gaya muku, ina da ilimin da zan fara fitar da ‘yan Najeriya daga kangin talauci.”

Na fi kowa cin WAEC 1976: Abokin takarar Atiku ya magantu kan batar takardunsa

A wani labarin, Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta, ya karyata rahotannin da ke cewa ba shi da takardar sakamakon kammala karatun sakandare na WASC.

Dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya bayyana cewa shi dalibi ne mai kwazo a matakin sakandare, inji rahoton jaridar The Nation.

Gwamna Okowa ya kara da cewa, shi ne ya fito a matsayin dalibi na biyu mafi kwazo a jarrabawar da ya rubuta a 1976.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel