An nemi Ma’aikaci an rasa tun da aka yi kuskuren aika masa albashin shekara 27

An nemi Ma’aikaci an rasa tun da aka yi kuskuren aika masa albashin shekara 27

  • A wani kamfani a kasar Chile aka aikawa ma’aikaci kudin da ya nunka albashinsa fiye da sau 200
  • Tun da wannan ma’aikaci ya tsinci dame a kala, sai aka neme shi aka rasa, har yau babu labarinsa
  • Diario Financiero da ta fitar da rahoton ta ce ma’aikacin ya rubutawa kamfanin takardar murabus

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Chile - Wani mutumi a kasar Chile ya zama abin labari bayan da ya tsere da ya fahimci an biya shi kudin da ya haura albashin da ya karba a duk wata.

Rahoton Diario Financiero ya ce ma’aikacin nan ya rubuta takardar ajiye aiki, sannan ya yi gaba, duk da ya yi alkawarin zai dawo da wannan kudin.

Wannan mutum da ba a san sunan sa ba, ya ji kamar ya yi nasara ne a caca domin kuwa a farat daya ya tashi da kudin da ya nunka albashinsa sau 268.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu : Tsohon Firaministan Japan da aka harba a ranar Alhamis ya rasu a Asibiti

Jaridar Mirror ta Ingila ta ce ma’aikacin yana aiki ne da kamfanin Cial masu aikin nama a Chile.

N75m a maimakon N220, 000

Da ma’aikacin ya fahimci 65,398,851 (£147,180.82) aka biya shi a karshen wata, a maimakon 500,000 (£444.95) da ya saba karba, sai ya yi batan-dabo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da Manajojin kamfanin suka lura sun yi kuskure wajen biyan albashin, sai suka tuntubi wannan mutumi da nufin ya dawo da karin kudin da aka yi masa.

Ma’aikaci
Ma'aikatan wani kamfani a ketare Hoto: ww.npr.org/Bloomberg
Asali: UGC

A nan ya shaida masu cewa zai je banki washegari domin ya ciro kudin, har yau babu labarinsa.

Ma'aikaci ya kauracewa ofis

Tun ranar ake jiran ma’aikacin ya zo ofis domin ya dawowa kamfani da kudinsu, abin mamaki sai aka ga wannan mutumi ya ki zuwa aiki bayan abin ya faru.

Manajojin kamfanin sun yi ta kokarin tuntubar shi amma abin ya faskara. Da aka yi dace aka same shi, sai ya bada uzurin barci ne ya dauke shi a lokacin.

Kara karanta wannan

Ragon layya N300K: Dillalai sun yi tagumi, jama'a ba sa zuwa sayen raguna

Kamar yadda ya yi alkawari da kansa, ma’aikacin ya ce daga baya zai je banki domin ciro kudin. Ana sauraronsa, sai kurum aka ji ya aiko takardar barin aiki.

Yanzu abin ya kai kamfanin Cial ya dauki hayar Lauyoyi, ya na kokarin karbe wannan kudi da aka yi tuntuben aikawa ma’aikacin, shi kuma tuni ya hau kansu.

Majalisa za ta binciki NNPP

A Najeriya, an samu rahoto cewa ana zargin NNPC da sauran masu ruwa da tsaki sun yi shekaru hudu, a duk wata sai an sace N70bn daga asusun man fetur.

Bayan watanni 12, majalisar tarayya ta ce N840bn sun yi batar dabo. Hakan ya sa Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya umarci a kafa kwamitin da zai yi bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel