Bidiyon mutumin da sana'arsa kenan yawo da dubban kudajen zuma a jikinsa
- A wani sabon salo, an samu mutumin da ke yawo da kudan zuma a jikinsa a matsayin sana'a
- Mutumin ya bayyana yadda yake samun nasarar manne kudajen zuma a jikinsa yake yawo dasu
- A cewarsa, ya kuma mayar da hakan sana'a kasancewar yana iya dauke zuma a gidaje kuma a biya shi
An ce harbin kudan zuma na iya haifar da kumburin jiki da tsananin zogi har ya kai ga rashin lafiyan da zai bukaci kulawar likita. Wannan yasa mutane da dama ke gudun kusantar wadannan kwari masu hadari.
Amma sabanin haka, an samu wani mutum da ya mayar da jikinsa wurin ajiyar kudajen zuma kuma sana'a mai romon riba, lamarin da ya kasance sabo ga jama'a.
Mutumin ya shahara a garinsu saboda iya yawo da yake da dubban kudajen zuma a jikinsa ba tare da wani kariya na jiki ba.

Kara karanta wannan
Rufe Makarantun Kaduna: Iyayen Ɗalibai Sun Ce Sun Fara Tura Ƴaƴansu Koyon Ɗinki Da Walda
Wani bidiyon YouTube na Afrimax ya nuna yadda mutumin ya aikata abin ban mamaki na yawo da kudan zuma.

Asali: UGC
Yadda yake yawo da kudan zuma
A cikin bidiyon, shahararren mutumin da ya lakaba wa kansa suna sarkin kudan zuma ya bayyana cewa domin sanya kudan su manne a jikinsa, da farko sai ya nemo sarauniyarsu kuma ya manne ta a jikinsa.
Da zarar ya samu nasarar yin haka, sauran kudajen zuman suna yin dandazo zuwa gare shi kuma su dasa sansani a jikinsa a kusa da sarauniyar ta su.
A cewarsa, yana sanya sarauniyar ne a jikinsa yadda ba za ta motsa ba, don haka yake daure ta da igiya a jikinsa saboda da zarar ta sauka a jikinsa sauran za su gudu.
Mutumin ya ce tun yana yaro yake manna dubban kudajen zuma a jikinsa.

Kara karanta wannan
Ba boye-boye: Mu ‘yan siyasa ne muka jefa kasar a cikin matsala – Rochas Okorocha
Yadda yake samun kudi a matsayin mai adana kudan zuma
Sakamakon shahararsa a garinsu, mutanen da kudan zuma ke damunsu suna neman taimakonsa wajen korarsu a muhallinsu, kuma yana karbar kudi domin yin wannan aikin.
Yana kuma sayar da zuma da kudan zuma ke samarwa a jikinsa.
Kalli bidiyon:
Murna ya lullube mahaifiyar tagwaye 'yan kwalisa da suka zama likitoci a rana daya
A wani labarin, Wasu samari kyawawa guda biyu, Chidimma Muogbo da Chinemerem Muogbo, wadanda tagwaye 'yan uwan juna ne sun kammala karatu a makarantar likitanci a matsayin likitoci.
Mahaifiyarsu, Uju Sussan mai digirin digirgir kuma babbar malama a Jami'ar Jihar Anambra ta Najeriya, ita ta yada labarin a shafinta na LinkedIn.
Baya ga taya 'ya'yanta maza biyu murna, mahaifiyar cikin alfahari ta kuma bayyana yadda suka fuskanci kalubale tare da dandamali daban-daban na kafofin sada zumunta da kuma tsarin tantancewa saboda kamanceceniyarsu.
Asali: Legit.ng