Titin Zuwa ‘Yan Kura Da Ke Birnin Kano Ya Cika Da Tarin Shara Da Ta Hana Masu Abin Hawa Bi Ta Kansa

Titin Zuwa ‘Yan Kura Da Ke Birnin Kano Ya Cika Da Tarin Shara Da Ta Hana Masu Abin Hawa Bi Ta Kansa

  • Sharar da ‘yan kasuwa ke zubarwa daga shagunansu ta yi sanadin cushe babban titin Court Road da ke Sabongari cikin birnin Kano
  • Titin dai na daga cikin manyan hanyoyin da ake bi zuwa kasuwar ‘Yankura da ma wasu sassa na birnin
  • Hukumar tsaftar muhalli ta jihar wato REMASAB, ta ce tana sane da lamarin, kuma za ta sanya mutanenta su kwashe sharar

Kano - Titin Court Road da ke cikin birnin Kano, ya cike da tarin shara wacce ta mamaye shi ta yadda masu ababen hawa basa iya bi ta kansa.

Titin wanda yake a yankin Sabongari, ya kasance daya daga cikin hanyoyin da a ke bi wajen shiga kasuwar Yankura dake cikin birnin na Dabo.

Wasu daga cikin ‘yan kasuwar da ke hada-hada a yankin, sun koka kan barazan kamuwa da cututtuka sakamakon sharar da aka jibge a kan titin. Sun bayyana hakan ne a zantawarsu da jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Radadin Cire Tallafi: Martanin 'Yan Najeriya Kan Aniyar Tinubu Na Raba N8000 Ga Gidaje 12m

Tarin shara a kan titin Kano
Shara ta cushe titin zuwa 'Yankura da ke birnin Kano. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan kasuwar ne suka tara sharar da kansu

Bayanai na nuni da cewa ‘yan kasuwar ne da kansu suka tara sharar saboda takamar cewa gwamnatin jihar za ta sa a kwashe.

Daga cikin ayyukan da gwamnati mai ci a yanzu ta yi, akwai ma’aikatan kwashe shara da ta sanya aikin kwashe ilahirin sharar dake cikin birnin Kano.

A cikin kwanakinsu na farko, sun yi nasarar kwashe akalla tan 600 na sharar da aka tara a wurare daban-daban na birnin.

REMASAB za ta sa a kwashe ilahirin sharar

Gwamnati mai ci a kwanakinta na farko a kan mulki, ta kuma sanar da dawo da Hukumar Tsaftar Muhalli ta jihar Kano (REMASAB), hannun gwamnatin jiha.

Kafin zuwan gwamnatin Abba, hukumar ta REMASAB ta kasance ba a hannun gwamnatin jihar ba.

Kara karanta wannan

Ja Ya Faɗo-Ja Ya Ɗauka: ‘Yan Majalisar Tarayya Sun Amince a Kashe Masu N70bn

Daraktan REMASAB, Ahmadu Haruna Danzago ya bayyana cewa hukumar na sane da lamarin kuma za ta tura mutanenta domin kwashe sharar a ranar Juma’ar nan.

Tarin shara a kan titin birnin Kano
Tarin shara a kan titi ya hana masu abin hawa bin titin zuwa 'Yankura. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Abba Gida Gida ya ce ko kadan bai yi nadamar rusau da yake yi a Kano ba

Legit.ng a baya ta kawo muku wani rahoto da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ko kadan babu nadama a ayyukan rusau da yake gudanarwa a jihar.

Mai magana da yawun gwamnan, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan a hirarsa da rediyon Freedom.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng