Yadda Mutanen Kabila Baki Daya Suka Musulunta a Hannun Sheikh Saidu Jingir

Yadda Mutanen Kabila Baki Daya Suka Musulunta a Hannun Sheikh Saidu Jingir

  • Ana cigaba da samun bayanai kan tarihin rayuwar mataimakin shugaban malaman kungiyar Izala mai hedkwata a Jos, Sheikh Saidu Hassan Jingir
  • Bincike ya nuna cewa Sheikh Saidu Hassan Jingir ya fara wa’azi tun yana matashi, inda ya yi gwagwarmayar yada addini da neman ilimi
  • Malamin ya taba bada labarin wani wa’azin da suka gudanar, mutanen ƙabilar Cakobo baki ɗaya suka musulunta, har da sarkin garin daga baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - A lokacin rayuwarsa, marigayi Sheikh Saidu Hassan Jingir, ya kasance ɗaya daga cikin fitattun malamai a Najeriya.

An haife shi a garin Cakobo a kusan shekarar 1948, tun kafin a samar da jihar Filato, inda ya tashi a cikin yanayi na karatun addini.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Wani bawan Allah ya faɗi ana tsakiyar sallah a masallaci, ya rasu a watan azumi

Jingir
Muhimman abubuwa kan marigari Saidu Jingir. Hoto: Hamza Muhammad Sani
Asali: Facebook

A wata hira da ya taba yi da Farfesa Mansur Sokoto da Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya wallafa a Facebook, malamin ya bayyana abubuwa da dama kan rayuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin hirar, Sheikh Saidu Jingir ya bayyana yadda ya yi gwagwarmayar neman ilimi da kuma yada addinin musulunci.

Jingir: Maganar musuluntar kabilar Cakobo

Sheikh Saidu Jingir ya fara kira zuwa ga addinin musulunci tun yana matashi, ya gudanar da wa’azi a yankuna daban-daban.

Daga cikin waɗanda suka karɓi musulunci sakamakon wa’azinsa akwai mutanen ƙabilar Cakobo baki ɗaya.

Ya ce lokacin da suka je garin Cakobo tare da Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir, gaba ɗayan mutanen garin sun musulunta.

Sai dai a lokacin, sarkin garin bai karɓi musulunci ba nan take, amma daga baya shi ma ya musulunta.

"Sarkin gari ya je wajen sarkin Jingir ya ce na zo ku karasa ni. Sai sarkin Jingir ya ce kamar ya mu karasa ka?"

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar malamin Musulunci, Farfesa Pantami ya tura sako ga Yahaya Jingir

Sai ya ce ku karasa ni mana tun da dukkan mutane na sun musulunta, ni ma zan karbi musulunci."

- Sheikh Saidu Jingir

Izala
Shugaban malaman Izala, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir. Hoto: Hamza Muhammad Sani
Asali: Facebook

Gwagwarmayar ilimi da wa’azin Saidu Jingir

Sheikh Saidu Jingir ya ce ya fara karatun addini ne a wajen mahaifinsa, ya haddace Alƙur’ani yana ƙasa da shekara 15 a duniya.

Ya kuma yi karatun Fikihu, Larabci da sauran littattafan addini a wurin mahaifinsa, wanda shi ma malami ne.

Marigayin ya bayyana cewa a da malamai suna nuna dattaku da tsoron Allah ba kamar abin da ke faruwa a yau ba.

Ya kuma kara da cewa a wancan lokacin a al’adu suna da tasiri sosai a cikin addini da rayuwar al'umma.

Ya ce tun kafin a kafa ƙungiyar Izala yana wa’azi, kuma da aka kafa kungiyar ya shiga cikinta don ci gaba da yaɗa addini.

Rasuwar Sheikh Jingir ta girgiza al’umma

Kara karanta wannan

Yadda rasuwar Sheikh Saidu Jingir ta girgiza gwamnoni da malaman Najeriya

Rasuwar Sheikh Saidu Jingir ta jefa al’umma cikin jimami, inda aka gudanar da addu’o’i da ta’aziyya a dukkan faɗin ƙasa.

Mabiya da dalibansa da dama sun bayyana cewa marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen yada ilimi da musulunci a Najeriya.

An gudanar da jana’izarsa a Jos, jihar Filato, inda aka birne shi kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Mutane da dama sun halarci jana’izarsa, ciki har da malamai, ‘yan siyasa, da shugabannin ƙungiyoyi na addini.

Daurawa ya yi ta'aziyyar Sheikh Jingir

A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya shiga sahun malaman addini da suka yi jimamin rasuwar Sheikh Saidu Jingir.

Haka zalika shugaban gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya, gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed sun yi ta'aziyyar rasuwar malamin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng