Allahu Akbar: Wani Bawan Allah Ya Faɗi Ana tsakiyar Sallah a Masallaci, Ya Rasu a Watan Azumi
- Allah ya yi wa wani bawan Allah ɗan kimanin shekara 52 Salihu Byezhe rasuwa bayan ya faɗi ana tsakiyar sallar Asuba a Abuja
- Wani mazaunin garin Gudaba, Musa Dantani ya ce Salihu ya ɗauki azumi kamar yadda aka saba bayan kammala sahur kafin rasuwarsa
- Tuni dai aka yi masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada yayin da mutanen garin ke ta masa addu'ar samun rahama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Wani mutumi ɗan shekara 52, Salihu Byezhe, ya faɗi yayin da yake yin sallar Subahi a ƙauyen Gudaba, da ke ƙaramar hukumar Kuje a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Wani mazaunin ƙauyen, Musa Dantani, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar Alhamis, 6 ga watan Ramadan, 1446H daidai da 6 ga watan Maris, 2025.

Asali: Original
Daily Trust ta tattaro cewa marigayin ya shirya kamar yadda aka saba domin tafiya masallaci, bayan ya gama Sahur (watau abincin ake ci kafin ketowar alfijir a watan Ramadan).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda mutumin ya faɗi a masallaci
Musa ya ce bayan ya kammala Sahur, ya yi alwala sannan ya nufi masallacin unguwar domin yin sallar Subahi tare da sauran al’ummar musulmi da ke zaune a yankin.
Ya ƙara da cewa yayin da ake tsakiyar sallah, sai kawai aka ga Salihu ya faɗi ƙasa babu zato babu tsammani a cikin masallacin.
Bayan da marigayin ya faɗi, mutanen da ke cikin masallacin sun gaggauta kai masa dauki, inda suka ɗauke shi suka nufi asibitin Kuje domin ya samu kulawa daga likitoci.
Allah ya yi wa mutumin rasuwa
Musa Dantani ya ce:
"Bayan an kabbara an fara sallah, kwatsam sai ya faɗi ƙasa, nan da nan musulmin da suka fito sallah a masallacin suka ɗauke shi zuwa asibiti.
"An tabbatar da cewa yana numfashi a hanya amma suna zuwa asibitin aka tabbatar da cewa rai ya yi halinsa."
Menene ya zama ajalin Salihu?
Dantani ya ƙara da cewa ɗan marigayin na ciki masallaci lokacin da mahaifinsa ya faɗi, kuma shi ne ya raka su asibiti, inda aka tabbatar da rasuwar mahaifinsa.
A cewar likitan da ya duba shi bayan an kai shi asibiti, hawan jini ne ya yi sandiyyar mutuwar Salihu Byezhe.
Wasu daga cikin abokansa sun tabbatar da cewa marigayin yana fama da hawan jini tun a baya, kuma yana shan magani a kai a kai.
An yi sallar jana'izar marigayin
Bayan rasuwarsa, an yi jana'izarsa da misalin ƙarfe 10:12 na safe a ranar Alhamis bisa koyarwar addinin Musulunci.
Dangin mamacin da abokansa sun bayyana shi a matsayin mutum na gari, mai mutunci da kuma son taimakon al’umma.
Sun ce rasuwarsa babban rashi ne ga ƙauyen Gudaba da ma danginsu baki ɗaya, tare da addu'ar Allah ji kan sa, ya gafarta masa kura-kuransa.
Ramadan: An fara ciyar da mabukata a Kano
A wani labarin, kun ji cewa an fara ciyar da mabuƙata a jihar Kano kuma ana sa ran musulmi akalla 90,000 za su amfana da abincin buda baki a Ramadan.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta bullo da shirin ciyar da azumi domin tallafa wa mabukata ta hanyar samar da abinci na buda-baki a duk tsawon watan azumi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng