Obasanjo @ 88: Tinubu Ya Jinjina, Ya Jero Alheran Tsohon Shugaban Najeriya

Obasanjo @ 88: Tinubu Ya Jinjina, Ya Jero Alheran Tsohon Shugaban Najeriya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jinjina wa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, a yayin cikar sa shekaru 88 a duniya
  • Ya bayyana Obasanjo a matsayin gwarzo da ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban Najeriya da kuma dunkulewar kasa
  • Tinubu ya roƙi Allah ya ƙara wa Obasanjo lafiya da tsawon rai domin Najeriya da Afirka su ci gaba da amfana da hikimarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi fatan alheri ga tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, a yayin cikar sa shekaru 88 a duniya.

A cikin sakon da ya fitar a ranar Laraba, 5 ga watan Maris 2025, Tinubu ya bayyana Obasanjo a matsayin gwarzo wanda rayuwarsa na da matukar alaka da tarihin Najeriya.

Kara karanta wannan

Seyi Tinubu da Minista sun dira gidan Buhari a Kaduna, an yada bidiyon

Obasanjo
Tinubu ya taya Obasanjo murnar cika shekaru 88 a duniya. Hoto: Bayo Onanuga|Kola Sulaimon
Asali: Twitter

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya fitar da bayanin shugaban kasar a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya ce Obasanjo ya taka muhimmiyar rawa a lokacin da ake bukatar jagoranci mai ƙarfi, kuma ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da dunkulewar kasa da zaman lafiya.

Gudunmuwar Obasanjo a tarihin Najeriya

Tinubu ya fadi rawar da Obasanjo ya taka yana soja, inda ya karbi takardar mika wuya daga kwamandan sojin Biyafara, Kanal Philip Effiong, wanda hakan ya kawo karshen yakin basasa.

Ya kuma tunatar da yadda Obasanjo ya zama shugaban mulkin soja bayan rasuwar Janar Murtala Mohammed a shekarar 1976.

Bayan haka, Tinubu ya bayyana yadda Obasanjo ya gudanar da zaben farar hula tare da mika mulki ga gwamnatin dimokuradiyya a 1979.

Bayan shekaru 20, a 1999, Obasanjo ya sake dawowa mulki a matsayin shugaban kasa na farar hula, ya jagoranci sabuwar dimokuradiyya da ke tafiya har zuwa yau.

Kara karanta wannan

An tsallake Tinubu, Atiku an ba Kwankwaso lambar karramawa a Najeriya

Rawar da Obasanjo ke takawa bayan mulki

Tinubu ya bayyana cewa ko da bayan barinsa mulki, Obasanjo na da tasiri sosai a harkokin siyasa da shugabanci, a cikin Najeriya da kuma kasashen duniya.

Ya ce Obasanjo yana taka muhimmiyar rawa a shawarwari kan zaman lafiya da warware rigingimu a Afirka.

Ko da yake yana da ra’ayoyi na daban a wasu lokuta, Tinubu ya ce hakan yana taimakawa wajen sa ido a kan shugabanci da kuma tsara manufofin gwamnati.

Obasanjo
Tsohon shugaban kasa, Obasanjo. Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

Tinubu ya yi wa Obasanjo fatan alheri

Shugaba Tinubu ya gode wa tsohon shugaban kasa bisa irin gagarumin gudunmuwar da ya bayar ga Najeriya.

Ya roƙi Allah ya ƙara masa lafiya da tsawon rai domin kasar nan da Afirka su ci gaba da amfana da hikima da basirarsa.

Daga karshe, shugaba Tinubu ya miƙa sakon taya murna ga Obasanjo a madadin gwamnatin Najeriya da al’umma baki ɗaya, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kaɗu da Allah ya yi wa babban sarki rasuwa a watan Ramadan

"Ina taya wannan babban jigo na Najeriya murnar cika shekaru 88. Allah ya ƙara maka lafiya da albarka."

Faransa ta cikawa Tinubu alkawari

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Faransa ta fara cika alkawarin yarjejeniyar da ta yi da shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A karkashin yarjejeniyar, kasar Faransa ta tattauna da shugabannin hukumar NDLEA kan horas da jami'ata a kan yaki da miyagun kwayoyi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng