Sheikh Jingir Ya Yi Dabarar Sanya Tinubu Kashe Naira Biliyan 33 a Aikin Titi
- Fara gyaran hanyar Kaduna zuwa Jos da Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ya yi da kansa ya jawo hankalin fadar shugaban kasa
- Malamin ya ce maimakon sukar gwamnati ko zanga-zanga, ya dauki matakin gyaran titin da kansa wanda hakan ya sa gwamnati ta shigo ciki
- Gwamnatin tarayya ta ware sama da Naira biliyan 287 domin gyaran hanyoyi 14 a fadin Najeriya, ciki har da hanyar Kaduna zuwa Jos
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato - Shugaban Izala, Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir, ya bayyana yadda ya jawo hankalin gwamnatin tarayya har ta dauki nauyin gyaran hanyar Kaduna zuwa Jos.
Malamin ya ce maimakon yin zanga-zanga ko sukar gwamnati, ya fara aikin ne da kansa domin zaburar da gwamnati ta dauki matakin gyara titin da ya dade yana cikin mawuyacin hali.

Asali: Facebook
Sheikh Jingir ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo da Yasir Haruna Muhammad ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kwanakin baya, Sheikh Jingir ya jagoranci gangamin tara kudi don gyaran titin, wanda a cewarsa, kokarin nasa ya sanya wasu jami’an gwamnati jin kunya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta sanya aikin cikin hanyoyi 14 da za a gyara a fadin Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC) ta ware fiye da Naira biliyan 287 domin gyaran wadannan hanyoyi.
Gwamnati za ta gyara hanyoyi 14
A wani taron Majalisar Zartarwa ta Kasa da aka gudanar, ministan ayyuka, Dave Umahi, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da ware kudi domin gyaran wasu hanyoyi 14.
Ministan ya ce wannan mataki na cikin shirin gwamnatin Tinubu na sake dubi, tsari da kuma fifita manyan ayyukan da aka gada daga gwamnatocin baya.
Daga cikin hanyoyin da za a gyara akwai titin Kaduna-Jos wanda za a kashe Naira biliyan 33.42, kuma shi ne titin da Sheikh Jingir ya fara gyarawa.
Hakanan akwai titin Agaye-Kachia-Baro a jihar Neja da za a kashe biliyan 22 a kansa, da titin Odukpani Junction–Apeti a jihar Kuros Riba wanda kudinsa ya kai biliyan 26.33.
Meyasa Sheikh Jingir ya fara gyaran titi?
A bisa alamu malamin ya fara aikin ne domin ya zama misali ga sauran shugabanni da kuma jama’a cewa idan an ga matsala, a nemi mafita maimakon zanga-zanga ko sukar gwamnati.
Malamin ya ce tun farko ya ga yadda titin ke cikin halin lalacewa, amma babu wanda ya dauki matakin gyara.
Saboda haka, malamin ya yi kokarin fara aikin da kansa tare da tara kudi daga al’umma wanda shi ma ya ba da N1m.
Wasu hanyoyin da za a gyara a Najeriya
Baya ga titin Kaduna-Jos, wasu daga cikin hanyoyin da za a gyara sun hada da:
- Titin Abeokuta-Ajibo zuwa Iyana Mosa a jihar Ogun – Naira Biliyan 10.89
- Titin Umuahia-Ikuano-Ikot Ekpene a jihar Abia – Naira Biliyan 14.37
- Titin Yola-Fufore-Gurin a jihar Adamawa – Naira Biliyan 11.81
- Titin Ikorodu-Shagamu a jihar Legas – Naira Biliyan 27.59
- Titin Nkomoro-Isu a jihohin Enugu da Ebonyi – Naira Biliyan 14.49
Haka zalika, an ware kudade domin aikin titin Gashi-Bayamari a jihar Yobe da titin Lamido a jihar Taraba, tare da wasu tituna a yankunan Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma.
An yi nasiha ga shugabannin Izala
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya yi nasiha ta musamman ga shugabannin kungiyar Izala.
Malamin ya bukaci Sheikh Jingir da Sheikh Abdullahi Bala Lau da su daina sukar juna saboda wani sabani da aka samu a tsakanin su.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng