'Japa': Abubuwa 10 da za Su Taimaki Dan Najeriya Mai Son Komawa Kasar Waje
Wani dan Najeriya da ya shafe shekaru da dama a kasar waje ya bayyana abubuwa 10 masu muhimmanci da za su taimaki masu son tafiya ketare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tunde Omotoye ya bayyana darussan rayuwa guda 10 da ya koya tun bayan zuwansa Canada shekaru 10 da suka gabata.
Tunde ya ba da shawarwari masu muhimmanci ga masu shirin yin hijira zuwa kasashen waje, musamman game da shirye-shirye da bincike kafin tafiya.

Asali: Twitter
A wannan rahoton, Legit ta tattaro muku abubuwa 10 da Tunde Omotoya ya wallafa a shafinsa na X domin su zamo jagora na tafiya kasashen waje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Fahimtar yanayin aiki a kasar da za ka tafi
Daya daga cikin manyan darussan da Tunde ya koya a rayuwarsa a Canada shi ne fahimtar yadda tsarin aiki ya ke.
A cewarsa, yana da muhimmanci mutum ya nuna kwarin gwiwa, kuma ya kasance mai magana cikin gaskiya. Ya ce hakan ya taimaka masa samun ci gaba cikin sauri.
2. Kwarewa kan harkokin kudi
Tunde ya bayyana cewa ilimin tattalin kudi ya zama dole ga mai son tafiya kasar waje daga Najeriya.
Ya ja hankali kan muhimmancin kula da tsarin bashi da lissafin kudi, saboda hakan yana shafar irin gida ko mota da za ka mallaka.
Haka zalika ya kuma shawarci wadanda ke shirin tafiya su fahimci yadda tsarin kudin kasar da za su je yake.
3. Fahimtar tsarin kiwon lafiya
Duk da ingancin kiwon lafiya a Canada, Tunde ya ce ya zama dole mutum ya fahimci bukatun lafiyarsa.
Ga dalibai, yana da kyau su bincika idan makaranta na ba su inshorar lafiya domin guje wa biyan kudi daga aljihunsu.
4. Shiryawa domin yanayin sanyi

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su
Tunde ya bayar da labarin yadda yanayin sanyi na farko da ya fuskanta ya kusa haddasa masa matsala.
A karkashin haka ya shawarci masu shirin tafiya zuwa kasashen da ke da yanayi mai sanyi su tanadi tufafin da suka dace.
5. Neman hanyoyin dogaro da kai
A cewarsa, akwai hanyoyin samun aiki wanda mutum ke samun dama ta hanyar:
- Tattaunawa da jama’a
- Hada kai da masana
- Shiga kungiyoyin kwararru da na neman aiki
6. Matsalar sufuri
Ga wadanda ba su da motoci, Tunde ya bayyana cewa dole ne su koyi yadda za su tsara tafiyarsu ta bas ko jirgin kasa.
Ya kuma bayyana cewa tafiya ta jirgi a cikin Canada na da tsada sosai fiye da wasu kasashen waje.
7. Kulawa da takardun izinin zama
Ya ja hankali kan muhimmancin kulawa da ranar karewar izinin zama, izinin aiki, ko takardar zama dan kasa.
Tunde ya tabbatar da cewa rashin kula da wannan na iya haifar da matsaloli masu tsanani ga baki.
8. Lura da tsadar rayuwa
Ya bayyana cewa rayuwa na da tsada sosai a kasashen waje, musamman a biranen kasar Canada da kewaye.
A kan haka ya shawarci masu shirin tafiya su tsara yadda za su iya tafiyar da rayuwarsu ta yadda za su fuskanci tsadar rayuwa.
9. Amfanin koyon wani yare
Kasancewar Canada kasa ce da ke amfani da Turanci da Faransanci, Tunde ya bayyana cewa koyon Faransanci na iya taimakawa wajen samun aiki, musamman na gwamnati da kamfanoni.
10. Bukatar cigaba da neman ilimi
Duk da cewa ba lallai mutum ya yi karatu a Canada ba kafin samun aiki, yana da kyau a kara ilimi daga jami’a ko kwaleji a kasar domin karin damar samun aiki mai kyau.
Rayuwar kasashen waje ba kamar yadda ake zato ba ce, amma ta na bukatar shiri mai kyau, bincike, da kuma jajircewa.
Kashim Shettima ya tafi kasar waje
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya isa kasar Switzerland domin taro.
Legit ta ruwaito cewa Sanata Kashim Shettima zai wakilci Najeriya ne a taron kuma ya samu rakiyar wasu ministoci da manyan jami'an gwamnati.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng