Kashim Shettima Ya Shilla Kasar Waje, Zai Wakilci Najeriya a Muhimmin Taron Duniya

Kashim Shettima Ya Shilla Kasar Waje, Zai Wakilci Najeriya a Muhimmin Taron Duniya

  • Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya yi tafiya zuwa birnin Davos na ƙasar Switzerland domin halartar taro kan tattalin arziƙi
  • Kashim Shettima zai wakilci Najeriya a wajen taron shekara-shekara kan tattalin arziƙin duniya (WEF) na shekarar 2025 da za a yi a birnin Davos
  • Shettima zai yi taro da shugabannin ƙasashen duniya daban-daban a yayin zaman da zai yi a birnin Davos
  • Mataimakin shugaban ƙasan wanda ya samu rakiyar manyan jami'an gwamnati da suka haɗa da ministoci zai dawo gida Najeriya bayan an kammala taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bar birnin tarayya Abuja zuwa birnin Davos na ƙasar Switzerland.

Kashim Shettima zai je ƙasar Switzerland ne domin wakiltar Najeriya a taron shekara-shekara kan tattalin arziƙin duniya (WEF) na shekarar 2025.

Shettima ya tafi Switzerland
Kashim Shettima ya tafi kasar Switzerland Hoto: @Stanley_nkwocha
Asali: Facebook

Stanley Nkwocha, mataimaki na musamman ga Shugaba Bola Tinubu kan harkokin watsa labarai da sadarwa na ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

"Za mu gyara inda ya kamata": Shettima ya lissafa muhimman ayyukan gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashim Shettima zai halarci manyan tarurruka

Stanley Nkwocha ya bayyana cewa Kashim Shettima zai haɗu da shugabannin duniya, manyan masu gudanar da harkokin kasuwanci, don tattauna halin tattalin arzikin duniya tare da nazarin hanyoyin da za a inganta shi.

A yayin zamansa a birnin Davos, mataimakin shugaban ƙasar zai yi taron haɗin gwiwa da wasu shugabannin ƙasashen duniya, tare da halartar tarurruka daban-daban da aka shirya.

Haka zalika, mataimakin shugaban ƙasar zai halarci liyafar dare da aka shirya wa shugabannin ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.

Yaushe Shettima zai dawo Najeriya?

Mataimakin shugaban ƙasar ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati, ciki har da ministan masana’antu, kasuwanci da zuba jari, Dr Jumoke Oduwole, da shugabar hukumar kula da zuba jari a Najeriya (NIPC), Aisha Rimi.

Kashim Shettima zai dawo birnin tarayya Abuja bayan kammala halartar taron tare da tawagar jami'an gwamnati da suka yi masa rakiya.

Mataimakin shugaban ƙasan dai ya sha wakiltar Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen muhimman tarurruka a ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Shettima ya bugi kirji a kan rashawa, ya ce za a magance matsalolin Najeriya

Karanta wasu labaran kan Kashim Shettima

Shettima ya yi wa ƴan Najeriya albishir

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Ƙashim Shettima, ya yi wa ƴan Najeriya albishir kan abin da zai faru a shekarar 2025.

Mataimakin shugaban ƙasan ya bayyana cewa ƴan Najeriya za su ji daɗin shekarar 2025 ta hanyar samun ci gaba sakamakon farfaɗowar da tattalin arziƙin ƙasar nan ya yi.

Kashim Shettima ya bayyana cewa ba wani lokaci mai tsawo za a ɗauka ba, ƴan Najeriya za su fara ganin canji domin tattalin arziƙin ƙasar nan yana kan hanyar dawowa bisa turba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng