Minista Ya Fadi Abin da Ya Kawo wa Gwamnatin Tinubu Tarnaki

Minista Ya Fadi Abin da Ya Kawo wa Gwamnatin Tinubu Tarnaki

  • Ministan Kudi, Wale Edun, ya bayyana cewa hauhawar farashi a Najeriya ya na kawo cikas ga gyare-gyaren tattalin arzikin gwamnatin tarayya
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da ya bayyana a gaban majalisa domin kare kasafin kudin da gwamnatin Bola Tinubu ta warewa ma'aikatarsa
  • Sai dai Sanatoci sun koka da manufofin gwamnati, sannan sun ki amincewa da ikirarin Ministan da na shugaban kasa a kan tattalin arziki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Ministan Kudi da Tsara Tattalin Arziki, Wale Edun, ya bayyana damuwa kan abin da ya kira hauhawar farashi mai tsanani a Najeriya.

Ya ce wannan na zama babbar kalubale wajen kokarin da ake yi na daidaita tattalin arzikin kasa da gwamnatin Bola Tinubu ke fafutukar yi.

Kara karanta wannan

An karrama Tafawa Balewa a Kwara, an sanya wa katafaren titi sunan Firayim Ministan

Tinubu
Gwamnatin tarayya ta ce hauhawar farashi ya zamo mata kalubale Hoto: Wale Edun
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, a cewarsa, hauhawar farashi na kawo cikas ga gyare-gyaren tattalin arziki da kuma kokarin bunkasa shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wale Edun ya fadi haka ne yayin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kudi, karkashin jagorancin Sanata Sani Musa na jam’iyyar APC a Abuja.

Gwamnatin Tinubu na son dakile hauhawar farashi

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Wale Edun ya ce akwai bukatar karfafa samar da abinci a cikin gida da kuma tabbatar da saukin samun abinci ga 'yan Najeriya.

Ya kara da cewa hauhawar farashin kayayyaki na rage karfin kudirin gwamnati a kan sassauta manufofin kudi daga Babban Bankin Najeriya (CBN).

Sanatoci sun nemi duba hauhawar farashi

Sanatoci sun bukaci gwamnatin tarayya ta sake duba hasashen 15% na hauhawar farashi da aka sanya a kasafin kudin 2025, suna bayyana hakan a matsayin abin da ba zai dore ba.

A lokaci guda, mambobin kwamitin sun yi sabani da ikirarin ministan cewa tattalin arzikin kasa na samun ci gaba a halin da jama’a ke ciki.

Kara karanta wannan

Sojoji su na ragargaza, an kai samamen dare a maboyar Boko haram

Sanatoci sun koka da manufofin Tinubu

A ziyarar Shugaba Bola Tinubu zuwa Abu Dhabi, Hadaddiyar Daular Larabawa, a karshen mako ya ce manufofin gwamnatinsa sun fara haifar da sakamako mai kyau.

Sai dai ‘yan majalisar sun samu sabani a kan hakan, musamman bayan Mista Edun ya kara nanata cewa an samu an tattalin arzikin ya faro farfadowa.

Amma Edun ya kafe a kan bakarsa na cewa tattalin arziki ya na inganta, amma ana samun cikas ne saboda bayanin da ya yi na cewa hauhawar farashi ya na kawo koma baya.

Tinubu zai turawa 'yan kasa kudi

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sanar da wani shirin tallafi mai muhimmanci domin rage talauci a Najeriya ta hanyar tura masu N75,000.

Gwamnatin ta bayyana cewa wannan tallafi wani bangare ne na matakan rage wahalhalun da mutane ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur da kuma sauran gyare-gyaren tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Shettima ya bugi kirji a kan rashawa, ya ce za a magance matsalolin Najeriya

Gwamnati ta ce za a yi amfani da fasaha wajen tabbatar da cewa kudin ya isa hannun wadanda suka cancanta kai tsaye, tare da yin alkawarin cewa tsarin zai kasance cikin gaskiya da adalci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.